Yayinda aka dawo domin ci gaba da buga wasannin UEFA Champions League a zagaye na biyu. BBabbn wasan da masu sha’awar kallon kwallon kafa zasu fi mayar da hankali a wannan satin shi ne wasa tsakanin Real Madrid da Napoli.
A tarihi, kungiyoyin biyu sun hadu sau biyar inda Real Madrid ta samu nasara a wasanni 4 sannan akayi kunnen doki daya.
- Murdyk Ya Jefa Kwallonsa Ta Farko A Chelsea A Karawarsu Da Fulham
- Antony Zai Iya Buga Wasan Man United Da Galatassary
Kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya bata taba samun nasara akan Real Madrid ba.
Kungiyar Napoli ce ke jan ragamar rukunin C na gasar ta UEFA yayinda Madrid ke binta a baya.
Madrid tana da ‘yan wasan da suka samu rauni kuma ba zasu buga wasan na yau ba da suka hada da Militao, David Alaba da kuma mai tsaron raga Thiabaut Courtois.