Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Turai (Uefa ) ta wanke Barcelona na wucin-gadi domin buga gasar cin kofin zakarun Turai ta 2023 zuwa 2024 a wani bincike da hukumar ta Uefa ke yi kan zargin da aka yi wa kungiyar na biyan kudade ga shugaban alkalan wasa.
A watan Maris ne UEFA ta tabbatar da cewa tana duba yiwuwar biyan kudaden da Barcelona ta biya domin samun goyon bayan alkalan wasa sai dai tun a lokacin Barcelona ta musanta aikata laifin.
- Kasar Sin Na Goyon Bayan Shimfida Zaman Lafiya A Colombia
- Na Fi So Na Fito A Masifaffiya -Amina Miloniya
Yayin da aka bai wa Barcelona izinin shiga gasar zakarun Turai, UEFA tana ikon hukunta kungiyar a nan gaba amma daman binciken na Uefa ya zo ne bayan da ofishin mai shigar da kara na Barcelona ya gabatar da wani binciken laifuka a ranar 10 ga Maris. An yi zargin cewa Barcelona ta biya Yuro miliyan 8.4 ga tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasa na Spain da kamfaninsa na Dasnil 95, wato Jose Maria Enrikuez Negreira.
An tuhumi Barca da tsoffin jami’an kungiyar da Negreira da laifin almundahana da cin amana da kuma gabatar da takardar kasuwanci ta karya kuma bayanin kudaden, wanda gidan rediyon Ser Catalunya ya bayyana a watan Fabrairu, ya fito fili ne bayan wani bincike da hukumomin haraji
suka yi kan kamfanin Dasnil 95, mallakan Negreira.
Barcelona ta amince cewa kungiyar ta biya Dasnil 95, don tattara rahotannin bidiyo da suka shafi kwararrun alkalan wasa da nufin inganta bayanan da masu horon ‘yan wasa ke bukata
Kungiyar ta kara da cewa yin kwangilar rahotannin al’ada ce a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya sai dai yanzu ana jira aga nan gaba wanne irin mataki hukumar zata dauka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp