Wata babbar kotun Jihar Kano karkashin mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ta dage shari’ar, Mista Geng Quangrong, dan kasar China da ake zargi da kashe budurwarsa Ummukulthum Buhari mai shekaru 23 a gidansu da ke Jihar Kano.
An gurfanar da Quanrong ne kan zargin daba wa budurwarsa, wacce aka fi sani da Ummita wuka a dakinta.
- Har Kullum Kasar Sin Na Goyon Bayan Adalci Game Da Batun Falasdinawa
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Yadda ‘Yan Nijeriya Za Su Kauce Wa Komawa ‘Yar Gidan Jiya A Zaben 2023
An fara gurfanar da shi ne a kotun majistare mai lamba 30 da ke zaune a unguwar Sabon Gari, karkashin jagorancin alkali, Hanif Sanusi Yusuf.
A yayin da ake tuhumarsa, alkalin ya zargi Quanrong mai shekaru 47 da aikata laifin kisa, wanda ya saba wa sashe na 221 na kundin laifuka na penal code.
Sai dai a zaman da aka yi a yau Alhamis, wanda ake zargin ya bayyana ba tare da lauyan da zai kare shi ba.
Don haka ya roki kotun da ta dage shari’ar domin ya samu lauyoyin da za su tsaya masa.
Da yake mayar da martani, babban lauyan Jihar Kano, Barista Musa Lawan, bai yi tsokaci kan rokon da wanda ake kara ya yi na dage shari’ar ba.
Ya ce, “Tabbas wannan shari’a ba za ta ci gaba ba a yau ba tare da lauya ba, ya tsaya ga wanda ake tuhuma. A halin da ake ciki, muna neman a dage sauraren karar don bai wa wanda ake tuhuma damar samun lauya.”
Daga nan sai mai shari’a Ma’aji ya dage zaman zuwa ranar 4 ga watan Oktoba, 2022.