Shirin inganta mu’amala tsakanin mabambantan al’ummomi na MDD (UNAOC), ya yi maraba da amincewa da babban zauren MDD ya yi, da ayyana ranar 10 ga watan Yuni, a matsayin ranar tattaunawa tsakanin mabambantan al’ummomi ta duniya.
Cikin wata sanarwa, Miguel Moratinos, mataimakin sakatare janar na MDD kuma babban jami’in UNAOC, ya ce yana maraba da amincewa da majalisar ta yi da ayyana ranar tattaunawa tsakanin mabambantan al’ummomi.
- Masana’antun Samar Da Kayayyakin Masarufi Na Gudana Cikin Wani Yanayi Mai Armashi A Kasar Sin
- CMG Ya Yi Kyakkyawar Fita A Dandalin St. Petersburg Karo Na 27
Ya kuma godewa kasar Sin da sauran kasashe mambobin majalisar da sauran wadanda suka dauki nauyin gabatar da kudurin, bisa yabawa da suka yi da muhimmiyar rawar da shirin ke takawa wajen yayata bukatar kara fahimta da girmama juna tsakanin mabambantan al’ummomi da al’adu da addinai da kuma yadda ake daukar dandamalin tattaunawa na hukumar, a matsayin dandalin tattaunawa tsakanin gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu, ciki har da kungiyoyin al’umma da shugabannin addinai da matasa da kafafen yada labarai da masana fasahohi da ‘yan wasa.
Ya kuma yi kira ga al’ummomin kasa da kasa su yi murna tare da girmama bambamcin dake akwai tsakanin su da kare martabar dan adam da kuma kaucewa wariya.
Yayin zama na 78 na babban zauren MDD a ranar Juma’a ne aka amince da kudurin da Sin ta gabatar na ayyana ranar tattaunawa tsakanin mabanbantan al’ummomi ta duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)