Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a wajen taron UNGA karo na 80, inda ya bukaci a ba Nijeriya kujerar dindindin a Majalisar Tsaro.
Shugaban, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya gargaɗi cewa MDD za ta rasa tasiri idan ba ta dace da yanayin duniya na yanzu ba. Ya bayyana cigaban tattalin arziƙin Nijeriya a matsayin abin koyi ga ƙasashe masu tasowa.
- An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin
- Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80
Tinubu ya nuna damuwa game da rashin ci gaba a batutuwan da suka shafi makaman nukiliya, rikice-rikice, da matsalar Falasɗinu, inda ya bayyana cewa mafita mai ɗorewa ita ce tsarin ƙasashe biyu. Ya ce “mutanen Falasɗinu ba ƙananan mutane ba ne, su ma sun cancanci ‘yanci da mutunci kamar kowa.”
Dangane da tattalin arziƙi, Tinubu ya kira da a samar da sabon tsarin duniya na kula da bashin ƙasashe masu tasowa. Ya jaddada cewa Afrika, musamman Nijeriya, na da albarkatun ƙasa da za su taka rawa a fasahohin gaba, don haka wajibi ne a sarrafa albarkatun a gida domin samar da aiki da rage rashin daidaito.
A ƙarshe, Shugaban ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka kamar cire tallafin mai da sauya tsarin kuɗi, duk duk sanya shan wahala amma wajibi ne domin tabbatar da cigaba. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam, da haɗin kai da zaman lafiya, inda ya gargaɗi duniya da cewa babu wanda zai tsira sai idan duk mun tsira tare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp