A gabanin bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD, taron kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD wato UNHRC karo na 59 ya zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar dangane da muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam. Wannan ne karo na farko da aka zartas da kudurin ta hanyar tattaunawa a maimakon kada kuri’a. Kasar Sin ta gabatar da kudurin ne a shekarar 2017.
Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland ya yi karin bayani kan kudurin da cewa, kudurin ya sake nanata muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, tare da jaddada yadda ci gaba mai inganci kuma mai mayar da jama’a a gaban kome, yake taka muhimmiyar rawa kan kyautata jin dadin jama’a da kuma kara azama kan bunkasar hakkin dan Adam.
Har ila yau, kudurin da kasashe 42 ciki har da Kamaru da Pakistan suka gabatar cikin hadin gwiwa ya bayyana fatan kasashe masu tasowa. Wakilai daga kasashen Cuba, Bolivia, Habasha, Kenya sun bayyana cewa, kudurin zai kyautata kulawar da ake nunawa kan muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam da kuma kara azama kan kiyaye hakkin dan Adam ta hanyar samun bunkasa mai dorewa. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp