Gwamnatin Donald Trump ta sanar da dawo da tallafin USAID da ta dakatar a wasu ƙasashen duniya, kamar yadda rahotanni daga Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters suka tabbatar.
Wannan tallafi zai koma ne zuwa ƙasashe da suka haɗa da Lebanon, Syria, Somalia, Jordan, Iraƙii da kuma Ecuador, inda aka ce muƙaddashin shugaban hukumar USAID, Jeremy Lewin, ya aike da saƙo ga ma’aikatansa domin dawo da kwangilolin ayyukan da aka dakatar, musamman na yaƙi da yunwa.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
Haka kuma wasu majiyoyi sun bayyana cewa an dawo da aikin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) a yankin Pacific.
Wannan matakin na dawo da taimako ya biyo bayan matsin lamba daga wasu jiga-jigan gwamnatin Trump da kuma mambobin Majalisar Dokoki ta Amurka.
Sai dai har yanzu Amurka ta ƙi dawo da tallafin da ta ke bayarwa a Afghanistan da Yemen.
A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka, Tammy Bruce, akwai damuwa kan taimakon da ke iya faɗa wa hannun ƙungiyoyin Taliban da Houthi, waɗanda ke iko da mafi yawan yankunan waɗannan ƙasashe.
A baya-bayan nan, Hukumar Yaƙi da Yunwa ta Duniya (WFP) ta bayyana cewa katse tallafin Amurka tamkar “hukuncin kisa ne” ga miliyoyin mutane da ke fuskantar matsananciyar yunwa a faɗin duniya, musamman a yankunan da ake rikici.
Masu fashin baƙi na ganin wannan mataki na iya taimaka wa dubban mutane, amma kuma har yanzu ana buƙatar a duba inda taimakon ke zuwa don tabbatar da cewa yana taimaka wa mabuƙata ba tare da faɗa wa hannun ‘yan tada ƙayar baya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp