Uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da mataimakiyar sakatare janar na MDD kuma daraktar zartarwa ta hukumar kula da harkokin mata ta MDD Sima Bahous, sun ziyarci wurin nune-nunen ci gaban da aka samu wajen karfafawa mata da ‘yan mata gwiwa a bangaren fasahohin zamani, dake birnin Beijing na Sin.
An gabatar da nune-nunen ne a yau Talata a gefen taron shugabannin duniya kan harkokin mata. Peng Liyuan ta ce yayin da fasahar zamani ke saurin bunkasa, sabbin fasahohin sadarwa sun zama wani sabon karfin da mata da ‘yan mata za su iya cimma burikansu. Ta kara da cewa, kokarin Sin na bunkasa fasahohin zamani na sake kyautata rayuwar mata da ‘yan mata, da kirkiro damarmakin ci gaba a wannan zamani na amfani da fasahohi.
Madam Peng wadda wakiliya ce ta musammam ta hukumar UNESCO kan inganta ilimin mata da ‘yan mata, ta ce tana sa ran hada hannu da kowa da kowa wajen shiga wani sabon zamanin fasahohi mai cike da damarmaki da daukaka ci gaban mata a duniya.
A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata.
Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha)