Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta baiwa mata 500 manyan buhunan gyada da tallafin kudi a karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.
Uwargida, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta ce karamar hukumar Arewa ita ce ta fara cin gajiyar shirin da za a gudanar a daukacin kananan hukumomi 21 na jihar don taimaka wa mata wajen kasuwancinsu don dogaro da kai.
- Ambaliyar Ruwan Sama Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 3 A Jihar Kebbi
- Ambaliya: NEMA Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Mutane 22,202 A Kebbi
Ta bayyana hakan ne a lokacin da take raba kayan tallafi da kudade ga mata 500 da suka ci gajiyar tallafi a karamar hukumar Arewa ta jihar, wanda ya gudana a harabar karamar hukumar.
A wajen rabon tallafin, kowacce daga cikin mata 500 da suka ci gajiyar tallafin ta samu manyan buhunan gyada guda biyu na biredin gyada, don yin (Kuli-Kuli) da tsabar kudi Naira dubu goma (N 10,000). Ta kuma bayyana cewa, babban dalilin da ya sa aka ba su wannan tallafin shi ne don baiwa wadanda suka ci gajiyar tallafin damar tura ’ya’yansu a makarantun Boko da na addini a garuruwansu, inda ta jaddada cewa ilimi ba shi da wata tangarda, ginshikin rayuwa da ci gaban al’umma ne.
Sai dai kuma ta yi kira ga sarakunan gargajiya a jihar da su ba gwamnati goyon baya da hadin kan da ake bukata domin bunkasa fannin ilimi da inganci da sabbin abubuwa.
“Samar da ci gaban ilimi zai zama abin al’ajabi ba tare da sa hannun sarakunan gargajiya musamman hakimai”, inji ta.
Dan Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, a Mazabar Arewa, Hon. Nura Kangiwa ya godewa uwargidan gwamnan bisa wannan karimcin, inda ya ba da tabbacin cewa majalisar za ta ba gwamnatin gwamna Nasir Idris hadin kan da ya dace domin cimma burinta na ci gaba.
Mai-Arewa Kangiwa, Alhaji Yusuf Sulieman ya baiwa uwargidan gwamna Sarautar gargajiya na “Madugar Arewa, Shugabar Matar Arewa”, a lokacin da ta ziyarce shi a fadarsa.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Hafsat Yusuf ta nuna godiyarta ga uwargidan gwamnan bisa ba su tallafin kudi da buhunan gyada. Ta kara da cewa hakan zai kara habaka kasuwancinsu na Kuli-Kulin gyada a cikin Al’ummarsu. Haka Kuma ta tabbatar wa matar gwamnan cewa “za mu yi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace”, inji ta.