Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bi sahun masu fafutukar kare hakkin bil-Adama na duniya domin tunawa da ranar jin kai inda ta tallafawa majinyata dubu daya dake kwance a baban Asibiti da ke Karamar hukumar Tsafe.
Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Matar Gwamnan Zamfara kan kafofin yada Labarai da Sadaukarwar Zahara’u Musa ce ta bayyana haka a takardar da ta sa ma hannun ga manema labarai a Gusau.
- Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Rabon Tirelolin Taki 135 A Zamfara
- Bayan Fafatawa, Ƴan Ƙauye Sun Hallaka Ƴan Bindiga 37 A Zamfara
‘Acewar ta ,Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ziyarci majinyata da ke kwance a babban Asibitin Tsafe inda ta bayar da tallafin kudi Da kungiyar matan Gwamnonin Arewa ta samar.
A wani bangare na tallafin, an kuma bada tallafin kayan abinci ga mata sama dubu daya a garin Tsafe.
Bada Tallafin ga Mata yana daga cikin kudinrin gwamnatin mai gidanta gwamna Dauda Lawal ya ke kuma cika alkawari da yayi masu a lokaci Yakin neman Zabe.
Kuma yanzu haka gwamnatin mai gidana gwamna Dauda Lawal na kokarin bullo da shirye shirye na Tallafawa dama da Kananan Yara domin samun sukin kuncin rayuwar da akeci.