Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa ƙungiyoyin mata manoma a Jihar Nasarawa tallafin Naira miliyan 26 don bunƙasa aikin noma da kuma inganta samar da abinci.
Da ta ke jawabi a fadar Gwamnatin Jihar Nasarawa a Lafia, Uwargidan Gwamnan Jihar, Hajiya Silifat Abdullahi Sule, wacce ta wakilci Uwargidan Shugaban Ƙasa, ta bayyana cewa wannan tallafi yana da nufin inganta rayuwar mata da matasa manoma tare da tabbatar da wadatar abinci a jihar.
- ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
- Babu Matsalar Da Za A Fuskanta Idan Majalisa Ta Tsige Fubara – Wike
Ta ce, “Jihar Nasarawa tana da arziÆ™in Æ™asa mai albarka da gadon noma. Mata da matasa suna da rawar da za su taka wajen bunÆ™asa tattalin arziÆ™in jihar. Wannan tallafi zai ba su damar samun kayan aiki da horo domin su zama shugabanni a fannin noma.”
Hakazalika, ta buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin su yi amfani da shi yadda ya dace domin ci gaba da habaka harkokin noma a jihar.
A nata jawabin, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ayyukan Jin-Ƙai, Margaret Elayo, wacce aka wakilta ta bakin Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Emmanuel Yonah, ta gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa da Ma’aikatar Noma ta Tarayya bisa wannan tallafi.
Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi.
An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu.
Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp