Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Joba, Dame Patience Jonathan, ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, inda ta yi alƙawarin yaƙin neman zaɓe tare da Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu.
Ta bayyana hakan ne a Abuja bayan karramar da kamfanin Accolade Dynamics Limited ya ba ta na “Jagorar Mata ta Shekara,” inda ta ƙaryata jita-jitar cewa mijinta, tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, zai fito takara a 2027.
- Ka Da Mu Yanke Kauna Da Nijeriya – Jonathan
- Yadda Na Ji Bayan Faduwa Zaben 2015 – Jonathan
“Ba kawai nasan Remi Tinubu ne dalilin ita ce Uwargidan Shugaban Ƙasa ba, a’a, mun yi aiki tare tun lokacin da nake mataimakiyar gwamna, har zuwa lokacin da nake uwargidan gwamna,” in ji Uwargidan Jonathan.
Ta ambaci yadda Sanata Remi ta tallafa wa iyalanta a siyasance, musamman lokacin da Goodluck Jonathan ya hau mulki. “Ko da lokacin da mijina ke mataimakin shugaban ƙasa, Oluremi ta tsaya tare da mijinta ta goyi bayanmu. Don haka ba zan iya yin watsi da ƙawaye na ba.”
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma bayyana cewa ba ta da niyyar komawa fadar Shugaban Ƙasa, inda ta ce tana jin daɗin zaman lafiya da hutun da take yi a yanzu.
“Ba za ku sake ganina a fadar ba. Idan kun kira ni, ba zan zo ba,” ta ce. “Kuna ganin yadda na yi kyau? Saboda hutun kwakwalwa da nake samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp