Wakilin CMG ya yi hira da tsohon shugaban majalisar nahiyar Turai, kuma tsohon firaministan kasar Belgium, Herman Van Rompuy, a kwanan baya, inda tsohon shugaban ya nanata bukatar karfafa cudanya tsakanin al’adun bangarorin yammaci da gabashin duniya.
Herman Rompuy ya ce, ta hanyar cudanya, kowa zai iya koyon sabbin dabarun da yake bukata, kana za a iya tabbatar da fahimtar juna. A daura da haka, idan an yi watsi da damar cudanya da tattaunawa, to, tabbas za a samu abkuwar rikici da arangama, har ma zai kai ga barkewar yake-yake.
- Aston Villa Na Neman ÆŠaukar Marcus Rashford A Matsayin AroÂ
- AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Fafata Da Tunisiya A Wasannin Rukuni
Dangane da shawarar raya “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, Mista Rompuy ya ce, ana bukatar tabbatar da saukin jigilar kayayyaki tsakanin kasashe daban daban, gami da ingancin cinikin duniya, ganin yadda suka jibanci wadatar al’ummun kasashen duniya. Saboda haka, yana goyon bayan duk wani matakin da zai amfanawa karfafar hadewar sassan duniya.
Ban da haka, tsohon dan siyasan na nahiyar Turai ya yi tsokaci kan shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da yunkurin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da ingancin cudanyar al’adu a duniya, inda ya ce, shawarwari sun nuna burikan da ake neman cimmawa a kasashe masu sukuni, da wadanda ke kan hanyar tasowa baki daya. Ya ce, dukkan kasar Sin da kasashen Turai za su iya samar da gudunmowa ga yunkurin cimma wadannan manyan burika masu muhimmanci. (Bello Wang)