A watan Satumba ne Faransa za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa a hukumance, kamar yadda Shugaba Emmanuel Macron ya sanar, hakan kuma ya sa Faransa ta zama ƙasar G7 ta farko da ta yi hakan.
A wani saƙo a shafin ɗ, Macron ya bayyana cewa a wani zama da za a yi a zauren Majalisar da ke New York ne za a ayyana hakan a hukumance.
“Buƙatar gaggawa a yau ita ce a kawo ƙarshen yaƙin Gaza a kuma samu kuɓutar da farar hular da ke zirin. Zaman lafiya abu ne mai yiwuwa. Muna buƙatar a gaggauta tsagaita wuta, a saki mutanen da ke tsare a kuma kai wa mutanen Gaza gagarumin agajin jin ƙai,” kamar yadda ya rubuta.
- Masallacin Ƙudus Na Musulmin Duniya Ne – Mabiya Shi’a
- Nijeriya Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Ake Kai Wa ‘Yan Jarida A Gaza, Ta Yi Kira A Gaggauta Tsagaita Wuta
Jami’an Falasɗinawa sun yi maraba da matakin Macron yayin da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce matakin kamar nuna goyon baya ne ga masu ta’addanci sakamakon hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da Hamas ta kai kan Isra’ila.
Amurka, da kakkausar murya ita ma ta yi fatali da sanarwar Macron, in ji Sakatare harkokin wajenta Marco Rubio, yana bayyana matakin a matsayin “ganganci”.
G7 ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki wadda ta ƙunshi Faransa da Amurka da Birtaniya da Italiya da Jamus da Canada da kuma Japan.
Isra’ila ba ta amince da samar da kasar Falasdinawa ba a Gabar yamma da Kogin Jordan da Gaza, saboda a tunaninta, kasar za ta zama barazana ga kasantuwar Isra’ila.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya rubuta wani sakon ɗ cewa: “Samar da ƙasar Falasɗinawa a irin wannan yanayi zai samar da wata kafar ruguza Isra’ila – ta kasance cikin tashin hankali. Mu gane wani abu: Falasɗinawa ba ƙasa suke so ba kusa da Isra’ila, suna neman ƙasa ne a maimakon Isra’ila.”
Su wane ne suka amince a samar da ƙasar Falasɗinu?
A yanzu, fiye da ƙasashe 140 cikin mambobin Majalisar ɗinkin ɗuniya 193 ne suka amince a samar da ƙasar Falasɗinawa. ciki har da mambobin ƙungiyar ƙasashe Larabawa da ke Majalisar ɗinkin ɗuniya da ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi da kuma ƙungiyar yan ba-ruwanmu wadanda ba su nuna matsayarsu ba.
Wasu ƙasashen Turai na daga cikinsu har da Sifaniya da Ireland da Norway wadda ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa a Mayun 2024. Gabanin haka, ƙasashen Turai ƙalilan ne suka yi haka galibinsu a 1988.
Sai dai babbar mai mara wa Isra’ila baya, Amurka da ƙawayenta har da Birtaniya da Australiya ba su amince da yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa ba. Australiya ta nuna cewa watakila za ta yi haka ne domin ita ma ta shiga sahun masu goyon bayan maslahar ƙasa biyu.
Me ya sa wasu ƙasashen suka ƙi aminta da kafa ƙasar Falasɗinawa?
ƙasashen da suka ki amincewa da ƙasar Falasɗinawa galibi ba sun yi haka ba ne saboda rashin samun yarjejejiya game da matsugunni wanda Isra’ila ta amince da shi ba.
“ɗuk da cewa a baki tana nuna buƙatar a kafa ƙasar Falasdinawa, Amurka ta dage kan batun tattaunawar gaba da gaba tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa, abin da ke nufin bai wa isra’ila damar hawa kujerar na ƙi kan bukatun Falasdinawa,” in ji Fawaz Gerges, farfesa a ɓangaren diflomasiyya tsakanin ƙasashe da siyasar Gabas ta Tsakiya a jami’ar London School of Economics.
An soma tattaunawar zaman lafiya a shekarun 1990 daga bisani burin samar da ƙasa biyu, inda Falasɗinawa da Isra’ila za su iya zama gefe da gefe da juna a ƙasashe daban-daban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp