Jam’iyyar adawa ta ADC, ta ce wa Shugaba Bola Tinubu, wa’adinsa zai ƙare a shekarar 2027, tare da jaddada cewa ‘yan Nijeriya ba za su ƙara zaɓensa don yin wa’adi na biyu ba.
Jam’iyyar ta mayar da martani ne kan furucin Fadar Shugaban Ƙasa da ta ce Tinubu ba shi da niyyar ci gaba da mulki bayan shekarar 2031, inda ADC ta bayyana irin wannan magana a matsayin yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa kuma raina hankalin ‘yan ƙasa.
- Xi Ya Bukaci Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Yankin Xinjiang Ya Zama Mafi Kyau
- Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
ADC ta zargi shugaban ƙasa da gazawa wanda ya hakan ya haddasa taɓarɓarewar tsaro, talauci, da yunwa a ƙasar nan.
Ta ce jama’a na fama da ta’addanci, kashe-kashe, tsadar abinci, da haraji masu tsanani, yayin da gwamnati ta kasa kare rayuka da inganta rayuwar al’umma.
Jam’iyyar ta kuma soki shugabancin Tinubu kan batun kare ‘yancin ɗan Adam, inda ta ce ‘yan jarida ana muzguna musu, masu zanga-zanga ana dukansu, kuma kotu ba a bin umarninta a ƙarƙashin mulkinsa.
A cewar ADC, maimakon shirin sake tsayawa takara, gwamnati ya kamata ta mayar da hankali wajen amincewar jama’a, farfaɗo da tattalin arziƙi, da kuma rage raɗaɗin da talakawa ke fuskanta.
Haka kuma ta yi gargaɗin cewa a shekarar 2027, siyasa ba za ta kasance tsakanin APC da jam’iyyun adawa kawai ba, illa tsakanin jam’iyya mai mulki da al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp