Assalamu alaikum! Barka da kasancewa tare da mu a cikin wannan shafi namu da muke kawo batutuwa da kuma tattaunawa kan al’amura da suka shafi mata, Tare da ni Hafsat Moh’d Arabi. Inda yau na kawo muku wani batun da na san za ku ji dadin karanta shi, Allah ya sa a amfana da shi Amin.
Wacece Kyakkyawar Mace?
Hakika da yawan mutane kan kasa fahimtar manufa da nufi na wannan Kalmar, inda za ka ga in an ce kyakkyawar Mace da yawa sukan maida dubansu ga kyan fuska da kuma kyan sura wanda ba a nan gizo ke sakarsa ba. Za ka iya samun mace da kyau da sura ammai ba lallai ba ne ta amsa wannan sunan na kyakkyawar Mace kasancewar Matan da ke amsa wannan suna ‘Elegant Women’ a turance inda a hausance muke mishi lakabi da ‘Kyakkyawar Mace’ ko cikakkiyar mace kan zo da nagarta ta musamman wanda ba kowace Mace ke amsa sunan ba. Kafin na kai ga kawo wadan nan nagarta din, yana da kyau mu san Wacece Kyakkyawar Mace?
Cikakkiya Kuma Kyakkyawar Mace ita ce wacce ke tattare da alkairi, dadawa ga dukkan wadanda take tare da shi kasancewar tana tare da ‘inner beauty’ a fannoni daban-daban na rayuwarta ga wasu daga cikin nagartar ita wannan Macen:
- Dabi’u Da Tarbiyya: Ladabi da kuma Dabi’u masu kyau abubuwa ne masu matukar Muhimmanci daga cikin nagartar Kyakkyawar Mace. Za ka same ta da girmamawa tare da kulawa kan dukkan mu’amularta ga uwa uba kirki da kuma kaifin tunani.
- Nutsuwa Da Juriya: Dole ka sama mace kyakkyawa da Nutsuwa da hankali a kan dukkan al’amuranta, takan kasance kuma me Juriya kan dukkan halin Rayuwa da ta tsinci kanta ciki.
- Salon Tafiya Da Zamani: Cikakkiyar Mace Kyakkyawa za ka same ta ga tafiya da duk abun da zamani ya zo da shi musamman bangaren wayancewa, girki, kayan sawa da sauransu. Za ka same ta da irin nata ‘taste’ din na daban ko a bangaren ‘dress sense’ dinta ta san inta sa wannan kayan ta sa wannan mayafin ko takalmi wanda zai fito da shigarta ta yi kyau sosai. Ita kyakkyawar Mace ko Hijabi ta sa sai ka gan ta daban saboda komai nata daban take yin sa saboda ta san kanta ta san me zai amshe ta me zai mata kyau meye kuma ba zai karbe ta ba duk hanyoyin sarrafa kanta ta san su ta hanyoyi daban-daban.
- Fahimtar Yanayi: Acikin nagartar Kyakkyawar Mace za ka same ta da saurin fahimta. Ko ya in kana tare da ita za ta famice ka da yanayinka ya sauya, haka kuma tana da fahimta wajen sauya maka yanayin ka zuwa farin ciki in kana cikin damuwa saboda saurin fahimta irin tasu. Kuma ko da ka saba musu ko ba ta mata rai tana iya danne dukkan damuwarta yadda ba lallai makusancinta ya gane tana cikin damuwa ba kasancewar ta san hanyoyin sarrafa kanta kan al’muran rayuwa.
- Hankali Da Ilmi: Ilmi na da Muhimmanci wajen Kyakkyawar Mace tana kuma daraja shi sosai, a kullum tunanin ta da lissafinta ya za ta san waccan ya za ta koya za ka same ta kullum cikin koyon Sabon abu take. Ko da hira za ka yi da ita za ka samu hirarta da Ilmi sosai a ciki tare da ma’ana. Wanda hakan ke matukar ba da gudunmawa wajen bude idonta da ci gabanta wajen fahimtar al’amuran duniya sosai.
- Fahimta Maikyau: Wata hanya da za ka gane Mace Kyakkyawa shi ne wajen Mu’amularta, ta hanyar magana ko rubutu za ka sama maganganunta da ma’ana sosai dan ba ta magana kasafai tana da nutsuwa wajen amfani da kalmomi masu ma’ana da kuma tsantsar Ilmi da Hankali. Tana gabatar da kanta a koda yaushe a mutunci, tsabta tare kuma da alkhairi. Duk wanda ya tattauna da ita sai ya ji dadin hakan.
Nan zan dasa Aya a wannan Batun namu wanda a wani satin ci gabansa zai zo In sha Allahu, Na gode!