• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Ce Kyakkyawar Mace?

by Hafsat Muh'd Arabi
2 years ago
in Ado Da Kwalliya
0
Wace Ce Kyakkyawar Mace?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Assalamu alaikum! Barka da kasancewa tare da mu a cikin wannan shafi namu da muke kawo batutuwa da kuma tattaunawa kan al’amura da suka shafi mata, Tare da ni Hafsat Moh’d Arabi. Inda yau na kawo muku wani batun da na san za ku ji dadin karanta shi, Allah ya sa a amfana da shi Amin.

Wacece Kyakkyawar Mace?

Hakika da yawan mutane kan kasa fahimtar manufa da nufi na wannan Kalmar, inda za ka ga in an ce kyakkyawar Mace da yawa sukan maida dubansu ga kyan fuska da kuma kyan sura wanda ba a nan gizo ke sakarsa ba. Za ka iya samun mace da kyau da sura ammai ba lallai ba ne ta amsa wannan sunan na kyakkyawar Mace kasancewar Matan da ke amsa wannan suna ‘Elegant Women’ a turance inda a hausance muke mishi lakabi da ‘Kyakkyawar Mace’ ko cikakkiyar mace kan zo da nagarta ta musamman wanda ba kowace Mace ke amsa sunan ba. Kafin na kai ga kawo wadan nan nagarta din, yana da kyau mu san Wacece Kyakkyawar Mace?

Cikakkiya Kuma Kyakkyawar Mace ita ce wacce ke tattare da alkairi, dadawa ga dukkan wadanda take tare da shi kasancewar tana tare da ‘inner beauty’ a fannoni daban-daban na rayuwarta ga wasu daga cikin nagartar ita wannan Macen:

  1. Dabi’u Da Tarbiyya: Ladabi da kuma Dabi’u masu kyau abubuwa ne masu matukar Muhimmanci daga cikin nagartar Kyakkyawar Mace. Za ka same ta da girmamawa tare da kulawa kan dukkan mu’amularta ga uwa uba kirki da kuma kaifin tunani.
  2. Nutsuwa Da Juriya: Dole ka sama mace kyakkyawa da Nutsuwa da hankali a kan dukkan al’amuranta, takan kasance kuma me Juriya kan dukkan halin Rayuwa da ta tsinci kanta ciki.
  3. Salon Tafiya Da Zamani: Cikakkiyar Mace Kyakkyawa za ka same ta ga tafiya da duk abun da zamani ya zo da shi musamman bangaren wayancewa, girki, kayan sawa da sauransu. Za ka same ta da irin nata ‘taste’ din na daban ko a bangaren ‘dress sense’ dinta ta san inta sa wannan kayan ta sa wannan mayafin ko takalmi wanda zai fito da shigarta ta yi kyau sosai. Ita kyakkyawar Mace ko Hijabi ta sa sai ka gan ta daban saboda komai nata daban take yin sa saboda ta san kanta ta san me zai amshe ta me zai mata kyau meye kuma ba zai karbe ta ba duk hanyoyin sarrafa kanta ta san su ta hanyoyi daban-daban.
  4. Fahimtar Yanayi: Acikin nagartar Kyakkyawar Mace za ka same ta da saurin fahimta. Ko ya in kana tare da ita za ta famice ka da yanayinka ya sauya, haka kuma tana da fahimta wajen sauya maka yanayin ka zuwa farin ciki in kana cikin damuwa saboda saurin fahimta irin tasu. Kuma ko da ka saba musu ko ba ta mata rai tana iya danne dukkan damuwarta yadda ba lallai makusancinta ya gane tana cikin damuwa ba kasancewar ta san hanyoyin sarrafa kanta kan al’muran rayuwa.
  5. Hankali Da Ilmi: Ilmi na da Muhimmanci wajen Kyakkyawar Mace tana kuma daraja shi sosai, a kullum tunanin ta da lissafinta ya za ta san waccan ya za ta koya za ka same ta kullum cikin koyon Sabon abu take. Ko da hira za ka yi da ita za ka samu hirarta da Ilmi sosai a ciki tare da ma’ana. Wanda hakan ke matukar ba da gudunmawa wajen bude idonta da ci gabanta wajen fahimtar al’amuran duniya sosai.
  6. Fahimta Maikyau: Wata hanya da za ka gane Mace Kyakkyawa shi ne wajen Mu’amularta, ta hanyar magana ko rubutu za ka sama maganganunta da ma’ana sosai dan ba ta magana kasafai tana da nutsuwa wajen amfani da kalmomi masu ma’ana da kuma tsantsar Ilmi da Hankali. Tana gabatar da kanta a koda yaushe a mutunci, tsabta tare kuma da alkhairi. Duk wanda ya tattauna da ita sai ya ji dadin hakan.

Nan zan dasa Aya a wannan Batun namu wanda a wani satin ci gabansa zai zo In sha Allahu, Na gode!

Labarai Masu Nasaba

Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AdoKwalliyaKyakkyawaMace
ShareTweetSendShare
Previous Post

Dubi Ga Rayuwar Uwargidan Shugaban Nijeriya, Oluremi Tinubu

Next Post

Ohanaeze Ndi Igbo Ta Yi Allah-Wadai Da Dakatar Da Emefiele

Related

Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4
Ado Da Kwalliya

Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

3 days ago
Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya
Ado Da Kwalliya

Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya

3 days ago
Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata
Ado Da Kwalliya

Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata

2 weeks ago
Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki
Ado Da Kwalliya

Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

3 weeks ago
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)
Ado Da Kwalliya

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

1 month ago
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata
Ado Da Kwalliya

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata

1 month ago
Next Post
Ohanaeze Ndi Igbo Ta Yi Allah-Wadai Da Dakatar Da Emefiele

Ohanaeze Ndi Igbo Ta Yi Allah-Wadai Da Dakatar Da Emefiele

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

July 1, 2025
HaÉ—akar Jam’iyyun Adawa Ba Ya ÆŠaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

HaÉ—akar Jam’iyyun Adawa Ba Ya ÆŠaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

July 1, 2025
Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

June 30, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta MiÆ™a SaÆ™on Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan ÆŠantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta MiÆ™a SaÆ™on Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan ÆŠantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.