An tabbatar da mutuwar mutane 12 yayin da hudu suka bace ya zuwa karfe 6 na maraicen yau Juma’a, bayan wata igiyar karfe ta tsinke yayin aikin gina wata gada a lardin Qinghai na arewa maso yammacin kasar Sin, kamar yadda hedkwatar hukumar ba da agajin gaggawa da ke kula da lamarin ta bayyana.
Ita dai igiyar karfen ta karye ce a yayin gudanar da wani aiki na amfani da karfi da misalin karfe 3:10 na goshin asubahin yau Juma’a a wurin da ake gina gadar a lardin Qinghai domin layin dogo na Sichuan zuwa Qinghai, da ke gundumar Jainca ta yankin Huangnan mai cin gashin kansa na kabilar Zang. Matsalar da aka samu ta yi sanadin fadowar hakarkarin gadar na karfe mai tsawon mita 108, inda ma’aikata 16 suka kasance a wurin lokacin da hadarin ya auku.
Jami’an ceto na yin bakin kokarinsu na nema tare da ceto wadanda suka bace, da kuma ba su kulawar kiwon lafiya, kana da bayar da tallafi ga iyalan da abin ya shafa. (Mai fasssara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp