Assalamu alaikum, malam da fatan kana lafiya, wasu tambayoyi nake rokon Malam da ya taimaka min da amsoshinsu in Allah ya sa malam ya san su, shin malam wai akwai wasu abubuwa uku da ake so mace ta fi mijin da za ta aura da su, sannan shi ma akwai abu guda uku da ake so ya fita da su?,
sannan akwai wadanda suka yi musharaka a kansu, da fatan malam ya sansu, kuma za a taimakamin da su, na gode.
To, ‘yan’uwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku: ta fi shi a kyau, ta fi shi kananan shekaru, ta fi son shi sama da yadda yake son ta.
Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku: ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta. Ana so su hadu a abubuwa uku: ya zama akwai yaren da yake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya.
Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za a samu jin dadin aure.
Don neman karin bayani ka nemi shirin minbarin malamai da na yi a freedom radio Kano na ranar: 3 ga Ramadhan 1434 A.H
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp