• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wadanne Sakamako Aka Samu Daga Cinikin Tsakanin Sin Da Kasashen Ketare

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Sin

Kwanan nan an fitar da sabbin alkaluman ciniki tsakanin Sin da kasashen waje, kuma abin lura shi ne, a farkon watanni 9 na bana, a karo na farko, kudin hajojin da kasar Sin ta fitar da su kasashen waje da ma shigo da su daga ketare ya zarce kudin Sin yuan triliyan 32, adadin da ya kai triliyan 30.8 a makamancin lokacin a bara. Ban da haka, a kowane rubu’i na wannan shekara, adadin ya zarce yuan triliyan 10, wanda kuma ya kasance na farko a makamancin lokacin a shekarun baya.

Alkaluman sun shaida cewa, a farkon watanni 9 na bana, kudin hajojin da kasar Sin ta fitar da su kasashen waje da ma shigo da su daga ketare ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 32.33, adadin da ya karu da kaso 5.3% kwatankwacin na bara. A yayin da ake fuskantar karin matakan kariyar ciniki da wasu kasashe suka dauka da ma kokarin farfado da tattalin arzikin duniya, yadda kasar Sin ta tabbatar da karuwar ciniki tsakaninta da kasashen ketare fiye da yadda aka yi hasashe, ba abu mai sauki ba ne.

  • Majalisar Dokokin Jigawa Ta Amince Da Ƙudirin Kafa Hukumar Wutar Lantarki
  • An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 20 Da Kafa Cikakkiyar Dangantakar Abokantaka Bisa Manyan Tsare-tsare Tsakanin Sin Da Italiya A Milan

In mun yi la’akari da yanayin ciniki a cikin gidan kasar, hajojin da kasar Sin ta samar suna da karfin takara sakamakon yadda ake samun cikakken tsarin samar da kayayyaki da saurin ci gaban fasahohi a kasar, matakin da ya aza tushen rika fadada kasuwanninsu a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Sai kuma in mun duba yanayin ketare, yadda bukatun kasuwannin ketare suka farfado ya samar da kyawawan sharuda ga kasar wajen fitar da kayayyakinta zuwa gare su. Rahoton da kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta fitar a kwanan baya ya kyautata hasashenta kan yawan cinikin hajojin na duniya cikin shekarar bana.

Ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare ya kuma samar wa kasa da kasa kayayyakin zamani masu inganci wadanda kuma ke kiyaye muhallin duniya. A halin yanzu, kasar Sin na fitar da motoci amsu amfani da lantarki da baturan Lithium da ma farantan samar da wuta daga hasken rana zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 200, wadanda ba ma kawai inganta samar da kayayyaki a duniya suka yi ba, har ma da taimakawa wajen saukaka matsalar hauhawar farashi, tare da bayar da babbar gudummawa wajen tinkarar sauyin yanayin duniya.

A takaice dai, yadda harkokin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare ya yi ta farfadowa, ya shaida ingancin tattalin arzikin kasar Sin, kuma shi ne dalilin da ya sa wasu hukumomin hada-hadar kudi na duniya, ciki har da Goldman Sachs, suka kyautata hasashensu kan bunkasuwar tattalin arzikinta a shekarar da muke ciki. (Lubabatu Lei)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Next Post
Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu

Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.