An gudanar da taron hadin kan ‘yan jarida na kasashen Afirka masu amfani da harshen Hausa a Niamey da ke kasar Nijar.
wannan taro dai, shi ne na farko da aka taba yi domin cimma wani buri da yake da alaka da masu harkaR yada labarai da kuma kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa da niyyar canza alakar yadda ake tafiyar DA harkokin sadarwa a Nahiyar Afrika.
- Turkiyya Da Nijar Na Tattauna Ƙulla Kawancen Soji Da Tattalin Arziki
- ‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Tuba A Kasar Nijar
Wata fitacciyar ‘yar jarida da ke aiki da babar tashar talabijin ta kasar Nijar, wato RTN (Tele Sahel), Hajiya Maryam Lawali Sarkin Arzen ta assasa kungiyar da za a gudanar da wannan aikin a karkashinta, wanda kuma take samun goyan hukumomi a kasar ta Nijar.
Babban manufar kafa kungiyar da kuma irin ayyukan da za a yi karkashin wannan tafiya shi ne, canza tunani ko alakar yadda ake yada labarai a kasashen Afrika masu amfani da harsunan gida, inda aka ba harshen Hausa babar dama fiye da kowane yare.
Taken wannan taron shi ne, “Inganta zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankali ta hanyar harshen Hausa da tabbatar da ‘yancin kai na kasashen Afrika,” wanda masana daga kasashe daban-daban suka tattauna kan wadannan batutuwa tare da ba ta mafita a kan wannan kudiri.
Taron ya samu halatar wakilai daga kasashe goma sha daya na Afrika da suke amfani da harshen Hausa wajen yada labarai, kimanin baki 2,500 aka gayyato da ‘yan jaridu 100 daga kasashe 11 da suka hada Nijeriya da Sudan da Chadi da Barki-Nafaso da Mali da Nijar da Benin da Kamaru da Togo da sauran kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa.
Shugaban Kasar Nijar, Janar Abdulrahamn Tiani ne ya bude taron na kwana uku da aka yi a baban dakin taron na Mahatma Gandi da ke cikin Birnin Niamey na kasar Nijar.
Janar Tiani wanda ya samu wakilicin Firaminista kuma Ministan Kudi da Tattalin Arziki na Kasar Nijar, Ali Lamine Zeine ya ce shugaban kasa yana tare da wannan taro dari bisa dari saboda muhimmancinsa da kuma kyawawan manufarsa.
Ya kara da cewa, hatta jawabin shugaban kasa an rubuta shi ne da harshen Faransa, amma saboda mahimmcin taron da kuma kungiyar dole aka umarci firaministan ya gabatar da jawabi da Hausa.
Ya ce gwamnatin ceton al’umma karkashin jagorancin Janar Tiani, tana tare da wannan tafiya kuma kofa a bude take domin ba da gudunmawa tare da fatan za a tattauna muhiamman abubuwan da za su amfani kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa domin samun nasara.
“Ina kira da babar murya ga ‘yan jarida su yi amfani da ilimi da basirar da Allah ya ba su wajen fadakar da al’umma halin da kasa take ciki, kuma su fadi gaskiya kan duk abin da suka gani wanda ba daidai ba, idan kuma an yi na daidai shi ma su fada” in ji shi.
Firaministan ya ce duk abin da mutun ya aikata gobe kiyama sai an tambaye shi kuma sai ya yi bayani, saboda haka dole a fadi gaskiya a wannan aiki da ya shafi rayuwar al’umma da ci gaban kasa da kuma al’umma.
Sannan ya yi tambihin irin matsalolin da aka samu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ta Nijar, inda ya ce an samu matsala da rashin fahimta tsakanin kasar tasu da kuma kungiyar habaka tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS), wanda har ta kai ga kasar Nijar ta janye daga wannan kungiya.
Hamza Almustapha ya nuna muhimmancin amfani da Hausa
Majo Hamza Al-Mustapha na daga cikin manyan bakin da aka gayyata domin halartar wannan taro, kuma ya yi jawabi game da muhimmancin yin amfani da harshen Hausa wajen tafiyar da al’amurran al’umma.
Ya kara da cewa ko lokacin zuwan Turawa sun iske al’umma suna da hankilinsu, suna tunaninsu suna da akidarsu, suna da alkalansu, suna da hukunci, suna da dokokinsu, suna karatu da rubutu, saboda haka babu wani abu da za a nuna wa wannan al’umma.
Al-mustapha ya ce idan wannan al’umma na san ta kwaci kanta daga hannu wadannan ‘yan mulkin mallaka, dole sai an canza yadda suka gurbata abubuwan da suka iska al’umma da su na asali masu kyau.
Haka kuma ya ja hankalin ‘yan jarida musamman wadanda suke amfani da harshen Hausa, inda ya ce suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen canza akalar yadda abubuwa suka tafiya a halin yanzu.
Ya ce ka da ‘yan jaridu su ba da kofa da za a yi amfani da su wajen canza gaskiya zuwa karya, ya ce hakki ne babba kan ‘yan jaridu su fadi abu yadda yake, saboda haka su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an samu nasarar wannan taro da kungiya da manufofin da aka tsara ta domin su.
Ya kara da cewa, al’ummar Nijar sun yi abin da ya kamata, saboda haka su kara jajircewa wajen bai wa shugabanin gwamnatin ceton al’umma ta sojoji karkashin jagorancin Janar Abdurahman Tiani domin a samu nasarar da ake bukata.
An dauko hanyar tabbatar wa al’umma da ‘yanci – Hajiya Naja’atu
Daya daga cikin ‘yan gwagwarmaya, kuma jigo a siyasar Nijeriya, Hajiya Na’ajatu Mohammad na daga cikin wadanda aka gayyata domin yin jawabi a wajen wannan taro.
Da take nata jawabin, Hajiya Naja’atu ta yaba da wannan taro wanda ta ce an dauki hanyar raba al’umma da bauta, da suka dade suna yi wanda Turawa makiyan Afrika suka kawo.
Ta kara da cewa daga ranar da aka dauke wa al’umma tunani da harshen da ba na su ba, to an bautar da su. Ta ce akwai mamaki ga mutum bakar fata mai kima da daraja, amma sai a ji yana cewa shi Bature ne wanda haka ba daidai ba ne.
“Yanzu yaki ya kare, yanci ba na rago bane, mutanen Nijar ba raggaye ba ne, sannan tsakanin Nijar da kuma Nijeriya a lokacin Daular Usmaniyya abu daya ne, saboda haka duk wanda ya ce yana san raba jini da tsoka, to ranmu yake nema, dole muma mu nemi nashi” in ji ta
Hajiya Naja’atu ta ci gaba da cewa duk wata gwamnati a duniya ana yin ta saboda amfanin ‘yan kasa, idan sojoji za su samar wa da ‘yan kasa abubuwan da suke bukata, Allah ya dawwamar da sojoji a kan mulki.
Kazalika, yar gwagwarmayar ta yi bayanin cewa arzikin da Allah ya yi wa Nahiyar Afrika ya sa Turawan mulkin mallaka suka hana wannan yanki sakat, tana mai cewa dole ne ‘yan Afrika su ci gajiyar arzikin da Allah ya yi masu.
Tattaunawar da aka yi da masana
Bayan kammala wannan taro, an shiga rana ta biyu da ta uku domin tattaunawa da masana kan makomar abubuwan da aka sa gaba karkashin kungiyar hadin kan ‘yan jaridu masu amfani da harshen Hausa a Afrika.
An tsara yadda masana za su gudanar da muhawara kan maudu’i daban-daban da suka shafi aikin jarida a wadannan kasashe kuma baki sun kasance cikin tattaunawar da kuma yin tambayoyi.
Aliyu Rabi’u daga tashar talabijin ta kasa wato NTA na daga cikin mahalarta taro kuma daya daga cikin wadanda za su tattauna da ‘yan jaridu a game da taron.
An ba shi maudu’i mai taken hadin kai a tsakanin ‘yan jaridu, inda ya yi bayanin dangane da abubuwan da suka shafi wannan taro. Bayan kammala jawabinsa aka tabka muhawara bisa kulawar ‘yar jarida daga gidan talabijin da rediyo ta kasa wato RTN.
Bayanan da Aliyu ya yi sun zama wani haske na kudirin da kungiyar ke da shi, na ganin kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa sun maida hankali domin canza alakar yadda suka gudanar da al’amuransu na yau da gobe.
Babu shakka bayanai sun gabata kan muhimmancin hadin kai kan duk wasu al’amurra da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye ba wai a aikin jarida kawai ba.
Shi ma Dakta Salisu na kungiyar kare hakkin Dan’adam, ya yi nasa jawabin ne kan yadda za a samar da ci gaba a tsakanin ‘yan jaridu da gwamnatoci da kungiyar domin cimma wancan manufa da aka samar da kungiyar.
Bayan kammala nasa jawabin an tabka muhawara a tsakanin mahalarta taro, kuma an samu matsaya kan hanyoyin da za a bi domin samun ci gaba a wannan tafiya da kuma abubuwan da za su ta so nan gaba.
Alhaji Tijjani Mustapha Mahadi, ma’akaci a fadar shugaban kasar Chadi, ya yi nasa jawabin ne kan batun da ya dabaibaye harkokin yada labarai wato labarun karya (fake News), inda ya dauki lokaci yana yi wa mahalarta taro bayani da kuma tarihin wannan matsala da hanyoyin maganin ta.
Ya kuma jefa kalubale ga ‘yan jaridu kan rawar da za su taka wajen rage wannan matsala ta labarun karya kafin wata rana ta zama tarihi.
Ya kawo misalai da dama, da irin yadda aka gudanar da aikin jarida a kasar Chadi wanda yana da bambanci a wasu kasashen Afrika musamman masu amfani da harshen Hausa, wanda shi ne ake son a dabaka a wannan kungiya da kuma taron.
An yi muhawara mai tsawo kan yadda jaddawalin tafiyar da wannan kungiya da kuma hanyoyin da za a bi domin tunkarar kalubalen da ‘yan jaridu da kafafen yada labarai suke fuskanta.
A jawabin rufe taro, shugabar kungiyar hadin kai ‘yan jaridu masu amfani da harshen Hausa a Afrika, Hajiya Maryam Lawal Arzein wanda ma’akaciya ce a gidan talabijin na kasa wato RTN, ta yi dogon bayani game da asassa kungiyar.
A cewarta, kafafen yada labarai musamman na Afrika suna fuskantar kalubale da yawa ta hanyar isar da sakon da ya kamata ‘yan kasa su sani.
“Kafa wannan kungiya zai taimaka wajen wayar da kan al’umma su kara sanin hakkin da ya rataya a kan su da kuma hakkin shugabannin kan mabiya, ‘ in ji ta.
Hajiya Maryam ta ce tana da burin ganin an kafa wata gidauniya da za ta rinka tallafa wa ‘yan jaridu musamman wadanda suka ajiye aiki kuma karfinsu ya kare ko mutuwa da makamantansu.
Tana mai cewa, sun gaji da gorin da ake yi wa ‘yan jaridu cewa makwadaita ne masu son abin duniya, inda har ake zargin ana yin amfani da su wajen lalata al’amurra.
Daga karshe ta bayyana cewa za a rika yin irin wannan taro sau biyu a shekara, inda take fatan cewa taro na gaba za a yi shi baban Birnin Tarayya Abuja na Nijeriya.