Tun daga lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa za ta gudanar da babban taronta na kasa da za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa, kallo ya koma kanta domin a ga irin wainar da za a toya saboda yawan ‘yan takarar da suka fito kuma kusan kowa ya ja tunga yana so ya zama dayan kwallin-kwal da jam’iyyar za ta tsayar.
Jam’iyyar ta gudanar da zaben fid da gwanin nata na takarar shugaban kasan ne daga Talata 7 zuwa Laraba 8 ga watan Yunin 2022, a dandalin taro na Eagle Skuare da ke Abuja.
Tun kafin fara gudanar da zaben, wasu daga cikin ‘yan takara wadanda suka hada da Ibikunle Amosun, Kayode Fayemi, Abubakar Badaru, Godswill Akpabio, Dimeji Bankole da sauran ‘yan takara mutum biyu sun janye daga takararsu, inda suka mara wa tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai kuma wadansu ‘yan takarar sun ki yarda su janye takararsu ga kowa, inda suka bukaci a gudanar da zaben wanda ya fi samun kuri’u shi ne ya samu nasara a karkashin jam’iyyar.
Domin samun maslaha, gwamnonin jam’iyyar APC na arewa sun fitar da wasu ‘yan takara guda biyar wanda daga bisani suka rage adadinsu ya koma uku domin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabi daya a cikinsu ya zama dan takarar da za a amince masa bisa maslaha.
‘Yan takarar aka darjen su ne Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Bola Ahmad Tinubu da Rotimi Amaechi.
Sai dai kuma, jim kadan da daukar wannan mataki, sai ga wasu ‘yan takara bakwai sun yi watsi da sunayen da gwamnonin APC suka aika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari guda biyar domin zaban dan takara na masalaha a cikinsu.
A wata tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa suka gudanar da Abuja sun ki amincewa da zaben wasu daga cikin ‘yan takarar, inda suka nemi a gudanar da zaben fid da gwani wanda daliget za su yanke musu hukunci.
Sauran ‘yan takarar sun hada da gwamnan Jihar Kuros Ribas, Ben Ayade da tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba da tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu da tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha da shahararren dan kasuwa, Tein Jack-Rich.
Sun bayyana cewa gwamnonin APC ba su tuntube su ba kafin yanke hukunci, wanda suka siffanta lamarin da wata alama na yunkurin watsar da sauran ‘yan takarar, musamman wadanda suka fito daga yankunan kudu maso gabas da kuma kudu maso kudu.
A kan wannan mataki da gwamnonin suka dauka, gwamnan Jihar Kogi, Bello ya je fadar shugaban kasa, inda ya gana da Shugaba Buhari. Ya dai yi watsi da matakin da gwamnonin APC suka dauka na ganin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ya koma kuda. Ya ce shugaban kasa ne kadai zai iya sa shi ya janye takararsa kai-tsaye.
Gwamnan ya bayyana wa wakilinmu na fadar gwamnati jim kadan bayan ganawarsu cewa Buhari yana goyon bayan a gudanar da sahihin zaben fid da gwani a cikin jam’iyyar APC.
Ya gargadi jam’iyyar da cewa za ta hada cikin rikici matukar aka cire sunansa daga cikin masu takarar zaben fid da gwani na shugaban kasa a cikin jam’iyyar.
Gwamno Bello ya ce ya zo fadar gwamnati ne domin ya bayyana wa Buhari dalilan da ya sa ya fita lokacin da yake ganawa da gwamnonin a ranar Litinin.
Ya kara da cewa ya shawarci gwamnonin APC kafin su yanke hukuncin kan zaben ‘yan takara guda biyar.
Ya jaddada cewa shi ne matashi da ‘yan Nijeriya suke bukata, kuma matukar idan aka gudanar da sashihin zaben fid da gwani na shugaban kasa shi ne zai yi nasara.
Da yake jawabin maraba a wurin zaben, shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya gargadi masu jefa kuri’a su yi kokarin zaben dan takarar da zai iya kaiwa ga nasara a babban zabe.
Adamu ya kara da cewa ya kamata wanda zai gaji Buhari ya kasance zai iya dorawa daga inda ya tsaya.
A cewarsa, ya kamata magajin Buhari ya kasance mutumin da zai iya bunkasa tattalin arzikin kasar da gudanar da kyakkyawan gwamnati a cikin al’ummar Nijeriya.
An dai bukaci ‘yan takarar su yi wa wakilai masu zabe dalilan da zai sa su zabe su.
Tinubu ya fara magana wanda ya siffanta kansa a matsayin mai hadin kan al’umma kuma wanda ake ta kiraye-kiraye ya fito taka a kasar nan.
Ya dai bukaci daliget su zabe shi bisa kwarewarsa da irin nasarori da ya samu kuma zai iya gudanar da kyakkyawan gwamnati a Nijeriya.
A nasa jawabi, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya siffanta gwamnatin Buhari a matsayin tubulin ci gaba kasar nan, sannan ya bukaci wakilai masu jafa kuri’a da su zabe shi domin dorawa daga inda Buhari ya tsaya domin bunkasa kasar nan.
Yayin da Ajayi Boroffice wanda ya janye wa Tinubu ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya kamata a bunkasa kasar nan ta hanyar kimiyya da fasaha da kuma kyawawan manufofin tattalin arziki.
Shi kuma gwamnan Jihar Kuros Ribas, Ben Ayade ya bukaci wakilai masu zaben fid da gwani na jam’iyyar APC su yi kokarin canza kasar nan.
Haka shi ma tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima ya yi alkawarin bunkasa harkokin ilimi da bai wa dalibai bashi domin gudanar da harkar iliminsu.
A nasa bangaren, gwamnan Jihar Ekiti, Fayemi wanda shi ma ya janye wa Tinubu ya bayyana cewa, shi ne dan takarar da ya cancanta a zabe domin zai hada kan al’ummar kasar nan.
A jawabisa, gwamnan Jihar Ebonyi, Dabid Umahi ya gode wa Shugaban Buhari wajen kokarin tabbatar da an gudanar da sahihin zaben fid da gwani a tsakanin ‘yan takara.
Shi kuma tsohon gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun wanda shi ma ya janye wa Tinubu ya bayyana cewa ya gamsu a fitar da dan takara ta hanyar masalaha, amma shi ya janye wa Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon ministan bunkasa yankin Neja Delta, Godwill Akpabio wanda ya janye wa Tinubu ya bayyana cewa shi ne ya fi cancanta ya zama shugaban kasa, amma dai shi ya janye wa Bola Ahmed Tinubu.
A nasa bangaren, tsohon shugaban majalisar wakilai, Dimeji Bankole wanda shi ma ya janye wa Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar samun ingantacciyar tattalin arziki a halin yanzu. A matsayinsa na masanin tattalin arziki yana da dubaru a kan yadda Nijeriya za ta bunkasa tattalin arzikinta.
Tsohon karamin ministan ilimi, Nwajiuba ba a ji duriyarsa a wajen zaben fid da gwanin APC ba duk da an kira shi ya zo ya gabatar da nasa jawabin ga galiget kan dalilansa na neman takarar shugban kasa.
Yayin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani wanda ya janye daga takararsa, ya bayyana cewa a yi wa yankin kudu maso gabas inda ya fito adalci.
Shi kuwa Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo, wanda shi ne na karshe daga cikin ‘yan takarar da suka yi jawabi ya tabbatar wa daligat na jam’iyyar cewa zai yi kokarin magance kalubalen da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.
Ya bukaci daliget su zabe shi domin Nijeriya ta samu kyakkyawan tsarin kiwon lafiya da harkokin ilimi da kuma samun shugabanci nagari.
A nasa jawabin, Shugaban Buhari ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC su hada kai tare da kaucewa rarrabuwar kai a tsakaninsu. Ya bayyana wa daliget cewa su yi kokarin zaben dan takarar da zai iya samun nasara a babban zaben 2023.
Shugaban kasa ya yi kira da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC da Abdullahi Adamu yake jagoranta da su ci gaba da hada kan ‘ya’yan jam’iyyar wajen kare manufofin jam’iyyar.
Kafin fara gudamar da babban taron, wasu ‘yan jarida da za su kawo rahoton kan abubuwan da ake gudana a wurin taro, sai da suka rasa kayayyakin aikinsu sakamakon rikici da ya farke a tsakaninsu da jami’an tsaro wanda takai har jami’an tsaro suka yi amfani da barkonun- tsohuwa a wurin.
An dai ga wasu jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a wurin taron. Wasu daga cikin suna sanye da kayan aiki, yayin da wasu kuma suke cikin kayan gida.
LEADERSHIP ya rawaito cewa jami’an hukumar EFCC sun zo Eagle Skuare ne domin duba safarar kudade ba bisa ka’ida ba, bayan da dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju ya rubuta wa hukumar wasika a kan su kula da babban taron jam’iyyar APC, domin ana zargin za a yi wasa da daloli a wurin taron.
Da yake gabatar da jawabin na musamman bayan samun nasarar lashe zaben fid da gwanin APC, Tinubu ya bai wa shugaban kasa Buhari hakuri na zaunar da shi tsawan lokaci a Eagles Skuare.
Tinubu ya lashe zaben ne da kuri’u 1,271 a cikin yawan kuri’u guda 2,322 da galiget suka jefa a lokacin babban taron jam’iyyar na musamman, wanda ya doke abokan hamayyarsa, Rotimi Amaechi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da suka sami kuri’u 316 da 235.
Tinubu ya gode wa matarsa da magoya bayansa da kuma wasu abokansa wadanda suka goya masa baya wajen ganin ya cimma burinsa.
Ya kara da cewa, “Ina bai wa Shugaba Buhari hakuri na zaunar da shi tsawon lokaci tun jiya a wurin taron.
“Amma wannan lokaci ne na daukan fansa kan dadewar sa a wurin nan.
“Ina jinjina wa uwargidan shugaban kasa. Babu wani abun da zai azabtar da shugaban kasa a wannan rana, sai dai wajen ganin jam’iyyar APC ta gudanar da sahihin zaben fid da gwani,” in ji Tinubu.
Yanzu dai dan takarar jam’iyyar zai fara shirin fuskantar babban zaben da zai kara da gwanayen sauran jam’iyyu da aka tsayar ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da ake sa ran gudanarwa idan Allah ya kai mu watan Fabarairun 2023.