‘Yan siyasar jihar Taraba na cikin firgici yayin da aka ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga a jihar sun gargade su day kar su fito yin gangamin yakin neman zabe a jihar.
Ko da yake tuni gwamnatin jihar ta soke yin gangamin yakin neman zabe a jihar, inda wannan gardadin na ‘yan bindingar, ya kara janyo fargaba a tsakanin ‘yan siyasar jihar.
Shugaban karamar hukumar Gassol Musa Abdullahi Chul, ya tabbatar da cewa, wasu sassa a karamar hukumar na karkashin karfin ikon ‘yan bindigar, ganin yadda suka kori mazauna yankunan sannan suka mayar da matsugunai da kadarorin jama’ar yankunan na su.
A makon da ya gabata, masu garkuwar sun sace Dagacin Gunduma tare da wasu mutum hudu, duk da cewa, tare da hadin gwiwar Jami’an tsaro, an kubutar da Mutum biyu amma sauran Ukun na Tsare a wurinsu.
Chul ya nuna damuwarsa kan yunwar da ke tafe a karamar hukumar ganin cewa damina ta kama amma manoma na jin tsoron zuwa gonakan su.
Chul ya ce, a kullum ‘yan bindigar na yiwa alummar yankin barazana, yanzu suna jira a fara gudanar da gangamin yakin neman zabe domin su sace wasu ‘yan takara a zaben 2023 don su karbi kudin fansa.
Ya sanar da cewa, a yanzu masu garkuwar sun gaji da sace talakawa ganin cewa ba sa samun wasu kudaden kirki na fansa, inda a yanzu, suke shirin fara sace manyan ‘yan siyasa.