A baya bayan nan hankula sun karkata ga tattauna tasirin kare-karen harajin fito da Amurka ta kakabawa sassan kasa da kasa, ciki har da wanda Amurkan ta sanyawa kayayyakin Sin dake shiga kasar. Masharhanta da dama na ganin matakin na Amurka na zuwa ne a gabar da ita kuma Sin ke kara fadada bude kofofinta bisa babban matsayi, tana yayata manufar gudanar da cinikayya cikin ’yanci, da kare tsarin cudanyar kasashe daban daban, da ingiza nasarar shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya” ko BRI a takaice.
Wani abun lura ma shi ne baya ga batun kakkaba haraji, ana ta ganin matakai daban daban, dake nuna burin kasar Amurka na sukar manufofin kasar Sin, na samar da ci gaban bai daya ga dukkanin kasashen duniya. Cikin wadannan matakai, akwai kiran manufofin Sin na raba ribar ci gabanta da “tarkon bashi”, da ma kaddamar da wani shiri mai lakabin “Sake Gina Duniya Mai Inganci” ko B3W, da gudanar da sauye-sauye kan manufofin Amurkan na samar da tallafin jin kai ga sassan kasa da kasa, wadanda ko shakka babu shaidu ne dake tabbatar da cewa Amurka ba ta yi watsi da yunkurinta na dakile shawarar BRI ta kasar Sin ba.
- Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?
- Jakadan Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Najeriya
To, amma abun tambaya a nan shi ne wane sirri ne shawarar BRI ke da shi, wanda ya sanya Amurka daukar matakan ganin bayanta, bayan da tuni kasashe sama da 150 suka riga suka rungumi wannan tafiya? Amsar hakan shi ne karkashin shawarar BRI, al’ummun duniya musamman ma na kasashe masu tasowa, da masu karancin ci gaba na cin matukar gajiyar tallafin kiwon lafiya, da na ilimi, da inganta noma, da makamashi, da sufuri, da binciken kimiyya da fasaha, da sauran fasahohin samar da ababen more rayuwa daga Sin. Ana ganin hakan a dukkanin sassan nahiyoyin Asiya, da tsakiyar Amurka, da Afirka da sauran su.
Ko shakka babu shawarar BRI ta zamo ginshikin haifar da moriya mai karko, da walwala, da juriya da kirkire-kirkire masu inganci, wadanda suka sanya ta zama mai matukar karbuwa ga daukacin al’ummun duniya.
A gabar da kare-karen harajin fito na Amurka ke gurgunta tsarin cinikayya na duniya, shawarar BRI ta Sin na samun karin karbuwa da muhimmanci ga duniya. Kuma tarihi zai ci gaba da fayyace karbuwar manufofin dake haifar da alfanu da al’ummun duniya, daga wadanda ke haifar da rarrabuwa da koma baya ga kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp