Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce shirin Japan na girke muggan makamai kusa da yankin Taiwan na Sin na da matukar hadari, kuma akwai bukatar kasashen dake makwaftaka da ita, da sauran sassan kasa da kasa su yi matukar sanya ido kan hakan.
Mao, ta yi tsokacin ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da take amsa tambaya da aka yi mata kan batun, tana mai cewa matakan Japan, na nuni ga aniyarta ta haifar da zaman doya-da-man-ja da gangan a shiyyar, tare da kokarin kunna wutar fito-na-fito da karfin soji.
Dangane da kalamai marasa dacewa na firaministar Japan Sanae Takaichi game da yankin Taiwan, jami’ar ta ce al’amari ne mai matukar hadari, tana mai kira ga kasashe makwafta da sauran sassan kasa da kasa, su yi matukar sanya ido kan batun.
Daga nan sai ta bayyana cewa, Sin ba za ta taba amincewa sassan Japan masu tsattsauran ra’ayi su mayar da tarihi baya ba, ba za ta kuma amince wasu sassan ketare su tsoma baki cikin batun yankin Taiwan ba, ko barin Japan ta farfado da manufar amfani da karfin soji a yankin. (Saminu Alhassan)














