A jiya ne, wakilan kasashen Sin da Kenya, suka halarci wani taron dandalin tattaunawa a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, inda suka tattauna hanyoyin da za a bi wajen neman zamanantar da kasashensu.
Taron tattaunawar na Hong Ting mai taken “hanyoyin zamanintar da kasashen Sin da Afirka” da aka gudanar a Nairobi, ya jawo hankulan mahalarta da suka hada da jami’an diflomasiyya, da masana, da ma’aikatan watsa labaru, inda ya bayyana burin da kasashen Sin da Afirka ke da shi na samun ci gaba cikin lumana.
- Masanan Kimiyya Na Kasar Sin Za Su Bunkasa Noman Rogo A Afrika
- Ranar ‘Yancin Kai: Tinubu Ya Bar Saudiyya Zuwa Guinea Bissau
Cibiyar tarihi da adabi ta kwamitin kolin JKS, da cibiyar nazari ta Xinhua, da ofishin kula da harkokin Afirka na kamfanin dillancin labarai na Xinhua ne suka shirya taron.
Babban darektan cibiyar kula da harkokin kasashen Sin da Afirka ta cibiyar nazarin manufofin Afirka, Dennis Munene Mwaniki ya bayyana cewa, bukatun kasashen Sin da Afirka na neman zamanantar da kasashensu sun dogara ne kan ingantattun ka’idoji na mutunta juna, da makomar bai daya da nuna sahihanci.
Dennis Munene ya lura cewa, kasar Sin ta kasance kan gaba wajen zamanantar da harkokin sufuri, da kiwon lafiya, da aikin gona, da masana’antu a Afirka, tare da samar da fa’ida ga mazauna kasashe. (Mai fassara: Ibrahim)