Dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Burra a Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Hon. Ado Wakili, ya rasu a ranar Juma’a biyo bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya.
Ya rasu kwanaki uku da kammala wa’adinsa na zama dan majalisar Dokokin jihar.
- Matar Aure Ta Watsa Wa Budurwar Mijinta Ruwan Zafi A Fuska A Bauchi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1 Da Garkuwa Da Sarakuna 2 A Jihar Bauchi
A sakon ta’aziyya da ya fitar, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y Sulaiman, ya ce radadin wannan rashin ya taba mambohin Majalisar da ma ma’aikatanta baki daya.
Kakakin ya nuna kaduwarsa matuka da jin labarin rasuwar Hon. Ado Wakili, inda ya misalta shi a matsayin dan uwansa kuma abokin aiki na kwarai da za a iya buga misali da irin gaskiyarsa da amanarsa.
Shugaban Majalisar ya yi addu’ar Allah ya jikansa da gafara, ya yafe masa dukkanin kura-kuransa.
LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa an an yi Jana’izar marigayin da misalin karfe 1:30 na rana a masallacin Juma’a na Gwallaga da ke cikin garin Bauchi a ranar Juma’a.