Wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, arangama ba zai iya warware batun nukiliyar kasar Iran ba, yana mai kira da a warware batun ta hanyar siyasa da diflomasiyya.
Zaunannen wakilin kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Li Song ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da kwamitin gwamnonin kasashe 35 na hukumar suka zartas da wani kuduri da ke matsawa Iran lamba kan nukiliyarta.
- Makarantu Masu Zaman Kansu Sun Koka Kan Kudaden Tafiyar Da Ayyukansu
- Farfesa Zaynab Alkali: Mace Ta Farko Da Ta Zama Marubuciyar Littattafai Daga Arewacin Nijeriya
Kasashen Sin da Rasha da Burkina faso sun kada kuri’ar kin amincewa da kudurin da Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus suka gabatar, yayin da kasashe 12 masu tasowa da suka hada da Afirka ta Kudu da Indiya da Masar suka kaurace.
Li ya kara da cewa: “Hakikanan gaskiya sun tabbatar da cewa, kirkiro sabani tsakanin juna, da kara tashe-tashen hankula a cikin kwamitin ba zai warware matsalar ba, sai dai zai iya haifar da tabarbarewar hadin gwiwa tsakanin hukumar da Iran, da kuma kara dagula lamarin,” yana mai jaddada cewa, matsa lamba ba tsarin diflomasiyya ba ce, kuma adawa ba za ta iya samar da mafita ba.
Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa muhimman hanyoyin warware matsalolin da suka shafi dakile matsalar sun ta’allaka ne a kokarin siyasa da diflomasiyya, da kuma yin hadin gwiwa mai ma’ana kan dandalin bangarori daban daban.
Li ya kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa da su kalli lamarin cikin “tsanaki da sanin ya kamata” tare da taka rawa mai ma’ana wajen warware batun nukiliyar Iran a siyasance. (Mohammed Yahaya)