Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Mu Hong, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Gabon, Brice Clotaire Oligui Nguema, a Libreville, babban birnin kasar, a ranar 3 ga watan Mayu, bisa gayyatar da shugaba Nguema ya yi masa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata.
Mu shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














