Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Hao Mingjin ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama a jiya Talata a Acrra, babban birnin kasar Ghana.
Bayan bikin rantsuwar, Mahama ya gana da Hao, wanda shi ne mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, sun tattauna hulda tsakanin kasashen biyu.
- Ɗansandan Da Ya Samu Lambar Yabo Saboda Ƙin Karɓar Cin Hancin $200,000 Ya Karɓi Musulunci
- Hadimin Gwamnan Kano Ya Rasu Kwana Ɗaya Bayan Rantsar Da Shi
A yayin ganawar, Hao ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga Mahama. Yana mai cewa, kasasr Sin tana mutunta dadadden zumuncin dake tsakaninta da Ghana, kuma tana ci gaba dagewa wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana bisa manyan tsare-tsare kuma na dogon lokaci.
A bana aka cika shekaru 65 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu. Hao ce, kasar Sin a shirye take ta yi amfani da wannan damar wajen inganta tuntubar juna da Ghana bisa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, da nufin daukaka dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Ghana zuwa sabon matsayi.
A nasa bangare, Mahama ya yaba da nasarorin da aka samu a dangantakar Ghana da Sin, kana ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta karfafa hadin gwiwa mai inganci tare da Sin a fannoni daban daban, don kara ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Mohammed Yahaya)