Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Qinghua ya halarci bikin rantsar da shugabar kasar Namibiya Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Windhoek, babban birnin kasar Namibiya a jiya Juma’a.
Peng, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, ya kuma gana da shugaba Nandi-Ndaitwah, inda suka tattauna dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
- Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya
- Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
A yayin ganawar tasu, Peng ya yi tsokaci mai zurfi game da dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Namibiya, inda ya bayyana cewa, a bana ake bikin cika shekaru 35 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Mista Peng ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi amfani da wannan damar wajen ci gaba da yin mu’amala mai kyau da kasar Namibiya, da kara amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a aikace, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, ta yadda za a ciyar da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Namibiya gaba, domin moriyar jama’ar kasashen biyu.
A nata bangare, Nandi-Ndaitwah ita ma ta yi tsokaci kan dangantakar Namibiya da Sin, inda ta gode wa kasar Sin bisa goyon baya da taimakon da ta dade take baiwa Namibiya, ta kuma bayyana fatan zurfafa hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.
A ranar Juma’a ne aka rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar kasar Namibiya bayan ta lashe zabe a bara.
“Aikin da ke gabana, shi ne kiyaye nasarorin da muka samu sakamakon ‘yancin kanmu daga dukkan bangarori da kuma tabbatar da cewa an ci gaba da aiwatar da ajandar bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummarmu da ba a kammala ba, tare da himmatuwa da jajircewa wajen samar da wadata bisa daidaito ga kowa da kowa.” a cewar Nandi-Ndaitwah a jawabinta na farko a matsayin shugabar kasa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp