Wakilin Sin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi tsokaci yayin zaman babban taro na farko na MDD, dangane da tunawa da ranar “Adawa da Dukkanin Siffofi Mulkin Mallaka a Duniya” a jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa, har yanzu duniya ba ta fita daga inuwar mulkin mallaka ba, kuma dole ne a yi tsayin daka kan yaki da dukkanin wata magana, ko aiki da ke kalubalanta, ko nuna burin hambarar da tsarin kasa da kasa bayan yaki.
Fu ya ce, a matsayinta na kasar da ta ci tura a yakin duniya na biyu, dole ne Japan ta zurfafa karatun baya game da laifukan da ta aikata a tarihi, ta kiyaye alkawuran da ta yi na siyasa game da batun Taiwan, kana ta daina tsokana nan take, ta kuma janye kalaman kuskure.
Jami’in ya kara da cewa, “Dole ne mu kare sakamakon nasarar yakin da Sinawa suka yi da mayakan Japan, da kuma yakin duniya na biyu na adawa da tafarkin murdiya, mu kuma kare tsarin kasa da kasa bayan yaki.”
Ya ce duk wata magana, ko aiki da ke kalubalanta, ko yunkurin hambarar da tsarin kasa da kasa bayan yaki, na iya haifar da tashin hankali a duniya, zai kuma iya haifar da mummunan bala’i ga daukacin bil’adam, don haka ya kamata a yi hattara, da kuma nuna adawa da hakan ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)














