Zaunannen wakilin Sin dake MDD, Fu Cong, ya gabatar da jawabi a gun babban taron MDD game da jefa kuri’ar kin amincewa jiya Laraba cewa, Amurka ba ta sauke nauyinta a matsayin babbar kasa ba domin ta dade tana jefa kuri’ar kin amincewa kan batun Falasdinu da Isra’ila.
Fu Cong ya bayyana cewa, rikicin Falasdinu da Isra’ila ya kwashe sama da shekaru 70 ana gwabzawa, zuriyoyin Falasdinawa sun rasa gidajensu kuma suna kaura, wannan rauni ne na ra’ayin jin kai. Kafa kasa mai cin gashin kanta, shi ne burin al’ummar Falasdinu, kuma shiga MDD a hukumance wani muhimmin mataki ne na wannan tsari a tarihi.
- Binciken CGTN: Kashi 80 Cikin 100 Sun Yaba Da Tasirin Sin A Duniya
- Xi Ya Amsa Wasikar Ma’aikatan Kamfanin Samar Da Karafa Na Smederevo Dake Serbia
A ranar 18 ga watan Afrilu ne Amurka ta ki yarda da batun, wanda ya murkushe mafarkin al’ummar Falasdinu na gomman shekaru, bangaren Sin ya yi bakin ciki sosai ga hakan.
Sau da dama Amurka na amfani da ikonta na kin amincewa a kan batun warware rikicin Falasdinu da Isra’ila. Bangaren Amurka ya riga ya jefa kuri’ar kin amincewa sau 5 tun daga barkewar rikicin Gaza na wannan karo. Amurka tana da taurin kai bisa muradunta da kuma siyasar shiyya-shiyya, matakin da ta dauka na nufin Amurka ba ta sauke nauyin dake kan wuyanta a matsayin wata babbar kasa.
Ana fatan Amurka za ta tsaya tsayin daka kan matsayin gaskiya da adalci, tare da shiga ayyukan tabbatar da adalci na kasa da kasa, da kuma taka rawar da ta dace wajen dakile yakin zirin Gaza da rage bala’in jin kai.(Safiyah Ma)