Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a jiya Laraba, yayin taro na 58 na kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin bil Adama na MDD, don bayyana ra’ayin kasar Sin kan halin da Palasdinu da Isra’ila ke ciki.
A cewarsa, daruruwan fararen hula sun yi asara sakamakon hare-hare ta sama da aka kaiwa zirin Gaza, kuma Sin na matukar adawa da hakan, tare da bayyana bacin ranta game da tabarbarewar matakin tsagaita bude wuta a wurin, wanda aka dauka bayan an sha matukar wahala. Ya ce abin da aka sa gaba cikin gaggawa shi ne kaucewa daukar ko wane irin mataki dake iya tsananta halin da ake ciki, ta yadda za a dakile barkewar bala’in keta hakkin bil Adama da jin kai mafi tsanani.
Chen ya kara da cewa, Sin na adawa da tilasawa fararen hula ficewa daga zirin Gaza. Kana tana goyon bayan shirin farfado da zaman lafiya a Gaza, wanda kasashen Larabawa ciki har da Masar suka gabatar, da farfado da zirin Gaza bisa ka’idar “Barin Palasdinawa su gudanar da harkokinsu da kansu” ba tare da bata lokaci ba.
Har ila yau, Chen ya jaddada cewa, ba za a iya warware batun Palasdinu ba, har sai an koma hanyar da ta dace, wato manufar “Kafa kasar Palasdinu da Isra’ila”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp