Kungiyar WTO ta kira babban taron kwamitinta karo na farko a shekarar 2025 a Geneva na Switerland jiya Talata. Yayin taron, wakilin Sin ya bayyana matukar damuwa kan karin harajin kwastam da Amurka ta yi wa sauran kasashe, wanda ya yi wa Amurkar mummunan tasiri, tare da yin kira ga mabambantan bangarori da su kiyaye manufar cudanyar bangarorin daban-daban bisa ka’idar da aka tanada ta daukar hakikanin matakai.
Wakilin dindindin na kasar Sin dake WTO Li Chenggang ya ce, manufar da Amurka ta dauka a kashin kanta ta saba da ka’idar WTO, kuma ta kara kamarin rashin tabbacin tattalin arziki da kawo cikas ga ciniki a duniya, tare da lalata manufar ciniki tsakanin bangarori daban-daban. Sin na bayyana matukar adawa da hakan, tare da kalubalantar Amurka da ta dakatar da manufar maras kyau.
Ban da wannan kuma, mambobin kungiyar fiye da 30 ciki hadda EU da Canada da Brazil da Rasha da sauransu sun bayyana rashin jin dadinsu game da hakan. Babbar jami’ar kungiyar madam Ngozi Okonjo-Iweala ta nuna cewa, ana fuskantar rashin tabbaci mai karin yawa a harkokin ciniki a duniya, kuma kamata ya yi mabambantan bangarori su yi amfani da dandalin kunigyar don kaucewar tsananatar sabanin tsakaninsu. (Amina Xu)