Jiya Laraba 21 ga wata a wajen taro na 53 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, wakili na musamman kan harkokin hakkin dan Adam na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Yang Xiaokun, ya bayyana matsayin gwamnatin kasarsa kan batutuwan da suka shafi Xinjiang, da Tibet, da Hong Kong, inda ya yi tir da abun da kasashen Birtaniya da Australiya da sauran wasu tsirarun kasashe gami da kungiyoyin da ba na gwamnati ba masu adawa da kasar Sin suka yi, wato amfani da kwamitin hakkin dan Adam na MDD don yayata labaran bogi, da nufin bata sunan kasar Sin.
Yang ya ce, a halin yanzu, tattalin arziki gami da zaman rayuwar al’umma na kara bunkasa a jihohin Xinjiang da Tibet, kana ci gaban hakkokin dan Adam a wuraren na cikin yanayi mafi kyau a tarihi. A yankin Hong Kong kuma, bayan da aka aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa, ana samar da cikakken tabbaci ga hakkoki gami da ‘yanci na mazauna wurin, har ma ‘yancin dokoki da tsaron kasa duk sun samu babbar kariya.
A wajen taro na 51 na kwamitin hakkin dan Adam na MDD, an ki amincewa da daftarin shirin da ya jibanci Xinjiang, kuma kasashe kusan 100 sun goyi bayan matsayin gwamnatin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Xinjiang da Tibet da Hong Kong, al’amarin da ya shaida matsayin kasa da kasa kan wannan batu. (Murtala Zhang)