Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga dukkanin sassa masu ruwa da tsaki da su kai zuciya nesa, su kaucewa furta kalamai da ka iya ta’azzara lamura, kana su kauracewa aiwatar da matakan ta da husuma, domin kaucewa kara tabarbarewar yanayin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Fu Cong, wanda ya yi kiran a jiya Litinin, yayin zaman MDD da aka gudanar game da batun aiwatar da sakamakon manyan tarukan MDD, da batun karfafawa, da aiwatar da sauye-sauye ga tsarin ayyukan majalisar, ya kuma koka game da yadda batun Falasdinu ya zamowa duniya “kadangaren bakin tulu”. Fu ya kuma yi kashedin cewa, a kullum tashin hankali a Gaza na ci gaba da tsawaita, tare da hallaka karin fararen hula, yayin da kuma a baya-bayan nan ya bazu zuwa kasar Lebanon, a gabar da cikakken yaki ke neman barkewa a Gabas ta Tsakiya baki daya.
- Imanin Sin Kan Ci Gaban Tattalin Arzikinta Zai Haifar Da Tasiri Mai Kyau
- Kare Hakki Da Rayukan Mutane Ba Batu Ne Na Siyasantarwa Ko Nuna Fuska Biyu Ba
Jami’in ya ce, “Muna kira da a martaba ikon mulkin kai, da tsaro, da ikon kare hurumin daukacin yankunan dukkanin kasashe, kana muna adawa da dukkanin wasu matakai da ka iya keta ka’idojin cudanyar sassan kasa da kasa, tare da sukar dukkanin wasu hare-hare kan fararen hula.”
Game da batun kasar Ukraine kuwa, jakadan na Sin ya ce, har yanzu abu ne mai wahalar gaske a yi hasashen kawo karshensa, don haka akwai bukatar dukkanin sassa masu ruwa da tsaki da su sanya batun wanzar da zaman lafiya da moriyar al’umma gaban komai, kana su rungumi tattaunawar dawo da zaman lafiya, da shawo kan dukkanin rikici ta hanyar siyasa. (Saminu Alhassan)