Shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar Tarayyar Turai (EU) Fu Cong ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai, su yi aiki tare don kiyaye masana’antu da tsarin samar da kayayyaki yadda ya kamata, da yin watsi da dakile tsarin, da ba da kariya da sunan tsaro.
Da yake jawabi a yayin taron shugabannin kasashen Sin da EU karo na biyar, kana taron tattaunawar tsoffin manyan jami’ai, Mr. Fu ya ce, kasar Sin ta bayyana karara a yayin babban taron wakilan JKS karo na 20 cewa, za ta tabbatar da dorewar manufofinta na cikin gida da waje cikin dogon lokaci, da kiyaye tsarin tattalin arzikin kasuwanci mai sigar gurguzu da bude kofa mai inganci.
Fu ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka, wajen yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da EU, kana tana sa ran kungiyar EU, za ta zama muhimmiyar abokiyar huldar kasar Sin ta hanyar zamani, da raba damar da babbar kasuwar kasar Sin ta samar, da manufar bude kofa ga waje, da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa.
Ya jaddada cewa, kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya mafi muhimmanci ga kungiyar EU, kuma ita ce babbar kasuwar bunkasuwa ga kamfanoni da dama na Turai. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)