Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai lura da harkokin Afirka Liu Yuxi, ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Gabon dake birnin Beijing a yau Laraba, inda ya gabatar da sakon ta’aziyyar rasuwar ministan wajen Gabon Michael Moussa Adamo.
Liu Yuxi, ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin, yana mika sakon jajen rasuwar Moussa, yana kuma bayyana matukar alhinin sa ga iyalan mamacin. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp