Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya gabatar da jawabi a taron kare zaman lafiya da tsaron duniya na kwamitin sulhu na MDD. Cikin jawabinsa, ya yi kira da a girmama mabambantan wayewar kai ta bil Adama, da mai da hankali kan samun ci gaba tare.
Zhang Jun ya ce, wurare na da mabambantan wayewar kai, amma bai kamata a bambanta wayewar kai cewar, wani ya fi wani daban kyau ba.
Duk wanda ke ganin wayewar kai tasa ta fi na wasu kyau, da tilastawa wasu canja wayewar tasu, rashin hankali ne, kuma zai haddasa illa ga kasa da kasa.
A tahirin duniyarmu, wasu kasashe sun yi mulkin mallaka a yankunan Asiya, Afirka da Latin Amurka, bisa ra’ayin “wayewar kai mafi ci gaba” da kuma ra’ayin nuna “fifikon farar fata”, lamarin da ya kawo barazana mai tsanani ga kasashen da abin ya shafa. A halin yanzu, wasu yammacin kasashen duniya na ci gaba da kawo sabani da rikice-rikice a tsakanin kasa da kasa bisa hujjar “neman dimokuradiyya da ’yancin kai da kuma adalci”.
Ya kara da cewa, girmama juna, da nuna adalci, da karfafa fahimtar juna su ne tushen tabbatar da dangantaka mai kyau a tsakanin kasashen duniya.
Kwanan nan, kasashen Saudiyya da Iran sun sanar da farfado da huldar diflomasiyya ta hanyar tattaunawa a birnin Beijing.
Lamarin da ya kasance abin koyi ga kasa da kasa wajen nuna girmama juna da daidaita sabani yadda ya kamata, da samar da damammaki ga kasashen yanki wajen yin hadin gwiwa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)