A yayin gudanar da taron tattauna al’amuran da suka shafi rangwamen kasuwanci na hukumar cinikayya ta duniya wato WTO a ranar 29 ga watan Afrilu, wakilin Sin ya zargi wasu jami’an gwamnatin kasar Amurka da yada jita-jita kan kasar Sin a fannin samar da kayayyaki fiye da kima, tare da yin Allah wadai da matakan Amurka na harajin kwastam da nuna bambanci ga kasa da kasa a fannin ba da rangwame da sauransu, wadanda suka saba wa ka’idojin hukumar WTO.
Kazalika, Sin ta yi kira ga membobin hukumar da su yi hadin gwiwa don kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da kuma tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban bisa tsarin hukumar WTO.
- Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno
- Ranar Ma’aikata: Gwamnan Kano Ya Biya Basussukan Fansho, Ya ƙirƙiro Sabbin Ma’aikatu
Kasar Sin ta bayyana cewa, wasu jami’an gwamnatin Amurka sun baza jita-jita kan kasar Sin a fannin samar da kayayyaki fiye da kima, inda hakan ya saba wa tsarin kasuwanci da na raya duniya baki daya, kana ta ce, Amurka tana nuna damuwa ce game da rauninta na yin takara a kasuwa, don haka take amfani da wannan batu don hana bunkasar kasar Sin, da kiyaye ra’ayinta na bangare daya, da ba da kariya ga cinikayyarta.
Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp