A farkon watan Fabrairun bana ne, sanannen ‘dan jairida na kasar Amurka Seymour Hersh, ya fitar da sakamakon bincikensa da ya bayyana cewa, hukumar leken asiri ta Amurka da sojojin kasar ne suka lalata bututun iskar gas na Nord Stream na Rasha, sai dai manyan kafofin watsa labarai na kasashen yamma ba su ce komai kan batun ba. Amma zuwa ranar 7 ga wannan wata, jaridar “The New York Times” ta kasar Amurka, da jaridar “The Times” ta kasar Birtaniya, da wasu kafofin watsa labarai na kasar Jamus, sun gabatar da sabbin rahotanni a sa’i daya cewa, wata kungiyar dake goyon bayan kasar Ukraine ce ta haifar da fashewar bututun.
Da yake zantawa da wakiliyar CGTN na CMG a baya-bayan nan dangane da batun, Seymour Hersh ya bayyana cewa, makasudin kafofin watsa labarai na kasashen yamma na yin hakan shi ne, baza jita-jita kawai, saboda kasar Ukraine ba ta da karfin daukar matakin lalata bututun.
Hersh ya kara da cewa, ya san sojojin ruwan kasar Ukraine ba su da sashen rage karfin matsi na jirgin ruwan karkashin ruwa. Kuma jami’in gwamnatin Amurka ya samar da bayanai ga jaridar “The New York Times” a daidai wannan lokaci ne domin karkatar da hankalin jama’a, ta yadda za a yi biris da cikakken rahoton da ya gabatar game da bututun iskar gas na Nord Stream. Ya ce hakika Amurka ta fara daukar matakin ne kafin bikin Kirismeti na shekarar 2021, inda mai ba da taimako ga shugaban kasar kan harkokin tsaron kasa, Jake Sullivan ya kira taro sau da dama, domin ya bukaci jami’an leken asirin kasar su gabatar da shirinsu na lalata batun Nord Stream. (Mai fassarawa: Jamila)