Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano, Nasiru Gawuna, ya bukaci magoya bayansa da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’unsu ga jam’iyyar APC a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 18 ga watan Maris.
Gawuna, mataimakin gwamnan jihar, yana karawa ne da babban abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP.
A wata sanarwa a ranar Lahadi a Kano ta bakin mai magana da yawunsa, Hassan Fagge, dan takarar ya ce, ta bin wannan hanyar ne kadai jam’iyyar za ta lashe dukkan mukaman siyasa a jihar.
“Ina kira da babbar murya ga magoya bayanmu da su fito kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri’a ga ‘yan takararmu a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a zabe mai zuwa.
“Muna yaba muku bisa jajircewa, kuma muna rokonku da ku fito a ranar Asabar 18 ga watan Maris ku zabi jam’iyyar APC.” Inji Gawuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp