Kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila Gareth Southgate ya ajiye aikinsa bayan jagorantar tawagar kasar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai karo biyu a jere. Tawagar ta Ingila ta sha kashi a hannun Sifaniya da ci 2-1 a wasan karshen da suka buga ranar Lahadi, da kuma wanda Italiya ta doke su a bugun finareti shekara uku da suka wuce.
A karshen shekarar nan ne kwantaragin kocin mai shekara 53 zai kare, inda ya ja ragamar kasar tasa ta haihuwa wasanni 102 cikin shekara takwas da ya yi yana jagorantar kasar. “A matsayina na dan Ingila mai cike da alfahari, bugawa Ingila wasa da kuma jagorantar ta alfarma ce a rayuwata kuma hakan ya fi komai a rayuwata, kuma na yi duk mai yiwuwa” in ji Southgate.
- Zargin Badakalar Naira Biliyan 423: Muna Nan Kan Rahotonmu Na Binciken el-Rufai – Majalisar Kaduna
- Zargin Badakalar Naira Biliyan 423: Muna Nan Kan Rahotonmu Na Binciken el-Rufai – Majalisar Kaduna
Tun daga 1966 da kocin Ingila Sir Alf Ramsey ya dauki kofin duniya, babu wani kocin tawagar ta maza da ya kai kungiyar wasan karshe a wata babbar gasa sai Gareth Southgate.
Ya kai Ingila manyan gasa hudu, ya kuma kai wasan kusa da na karshe a gasar Kofin Duniya a 2018 da kuma na kusa da dab da na karshe a 2022, sai dai ya fuskanci matsin lamba a wannan gasar, yayin da wasu magoya baya da dama suka yi amannar bai samu ‘yan wasan gaba isassu ba da zai tunkari gasar da su.
Wasu magoya bayan tawagar Ingila sun rika jifansa da kofinan roba bayan 0-0 da suka tashi a wasan da suka yi da Sloda enia, wanda ya basu damar tsallakawa zagayen ‘yan 16 amma daga baya sun dawo goyon bayansa lokacin da tawagar ta kai wasan karshe.
Wane Tarihi Southgate Ya Kafa?
Gather Southgate ya ja ragamar Ingila zuwa wasanni 102 ya kuma yi nasara a wasanni 61, wato ya samu kashi 59.8 cikin dari sauran wasanni 41 kuma, Ingila ta yi canjaras 24, sannan ta yi rashin nasara a wasanni 17.
Shi ne koci na uku a tarihin Ingila da ya fi kokari, ko da yake sauran masu horarwar biyu sun fi shi jan ragamar tawagar yawan wasanni sannan duka wasannin karshe da Ingila ta je a gasar Euro Southgate ne ya kai ta, gabaninsa babu wani kocin tawagar maza ta kasar da ya samu wannan nasara.
Shi ne mai horarwa na uku da ya dauki Ingila sama da wasanni 50 kuma yana cikin wadanda suka fi samu kaso mai yawa na nasara a kasar. Tuni hukumar kwallon kafa ta Ingila. FA, ta dukufa wajen neman wanda zai maye gurbinsa kafin watan Satumba da kasar za ta fara buga wasannin gasar cin kofin Nations League.