Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), Mr. Wang Yang ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Mozambique Esperanca Bias, da ma shugaban majalisar dattawan kasar Burundi Emmanuel Sinzohagera, a jiya Talata ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing.
A yayin zantawarsa da Esperanca Bias, Wang Yang ya ce, kasar Sin na fatan karfafa aminci, da tuntubar juna ta fannin siyasa da manyan tsare tsare tare da Mozambique, kuma kasashen biyu su fadada hadin gwiwarsu, tare da aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kana majalisar CPPCC na fatan inganta mu’amala tare da majalisar dokokin kasar Mozambique, don inganta tushen bunkasuwar huldar kasashen biyu.
A nata bangare kuwa, Madam Esperanca Bias ta bayyana godiya, kan goyon baya da taimakon da kasar Sin ke samar wa Mozambique a kullum, kuma ta yi fatan ganin karin nasarori a hadin gwiwar kasashen biyu.
A yayin zantawarsa da Emmanuel Sinzohagera kuma, Wang Yang ya ce, kasar Sin na fatan hada kai da kasashen Afirka, ciki har da Burundi, don tabbatar da shawarar raya duniya, da ma shawarar kiyaye tsaron duniya, a kokarin kiyaye moriyar kasashen Sin da Afirka, da ta kasashe masu tasowa.
Kaza lika majalisar CPPCC za ta karfafa mu’amala tare da majalisar dattawan Burundi, don ciyar da huldar kasashen biyu gaba.
Daga nasa bangaren, Emmanuel Sinzohagera ya ce, Burundi na dora muhimmanci sosai a kan bunkasa huldarta da kasar Sin, kuma majalisar dattawan kasar na fatan karfafa mu’amala, da hadin gwiwa tare da majalisar CPPCC, don kara bunkasa huldar kasashen biyu gaba. (Lubabatu Lei)