Wang Yi, darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a yau Litinin a nan birnin Beijing, inda ya yi kira da a yi kokarin gyara dangantakar kasashen Sin da Amurka wadda ta yi tsami.
Wang ya ce ziyarar ta Blinken a nan Beijing ta zo ne a wani muhimmin lokaci a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, inda ake bukatar zabi tsakanin tattaunawa ko gwabzawa, hadin gwiwa ko rikici.
Lura da cewa lokaci na tafiya haka ma alakar dake tsakanin Sin da Amurka. Wang ya ce canza tarihi ba zai yi tasiri ga makoma ba, haka ma wargaza dangantakar dake tsakanin kasashen biyu don a sake gina sabuwa.
Ya ce, “Dole ne mu nuna kyakkyawar hali ga jama’a, da tarihi da kuma duniya baki daya, tare da gyara dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka.” Ya yi kira ga bangarorin biyu da su maido da huldar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa tafarkin da ya dace, da kuma samar da hanya madaidaiciya ga Sin da Amurka don samun jituwa a sabon zamani.
A jiya ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dake ziyara a nan birnin Beijing.
A yayin shawarwarin, Qin Gang ya bayyana cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala mafi tsanani bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu, wannan bai dace da moriyar jama’ar kasashen biyu da begen kasa da kasa ba. Sin tana yin kokarin raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka ta zaman lafiya da amfani, Sin tana fatan kasar Amurka za ta maida hankali ga kasar Sin bisa hakikanin yanayi, da yin kokari tare da kasar Sin, da tabbatar da tushen siyasa na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da daidaita matsaloli ba zato ba tsammani cikin lumana yadda ya kamata. Kana kasashen biyu ya kamata su aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma a tsibirin Bali, da sa kaimi ga maido da dangantakarsu.
Qin Gang ya bayyana matsayin kasar Sin kan manyan batutuwan dake shafar moriyar kasar Sin, ciki har da batun yankin Taiwan, ya kalubalanci bangaren kasar Amurka da ya bi ka’idar Sin daya tak a duniya da hadaddun rahotanni uku da Sin da Amurka suka daddale, da cika alkawarinta na kin amincewa da ‘yancin yankin Taiwan.
Hakazalika kuma, bangarorin biyu sun zurfafa mu’amala da juna kan yadda za a raya dangantakar dake tsakaninsu da manyan batutuwan da abin ya shafa. (Mai Fassarawa: Zainab Zhang&Yahaya Babs)