• English
  • Business News
Thursday, July 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Harkokin Kasuwanci na Sin Wang Wentao Ya Gana Da Darakta Janar Ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Ministan Harkokin Kasuwanci na Sin Wang Wentao Ya Gana Da Darakta Janar Ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi

Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar

Ministan kula da harkokin kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao, ya gana da Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayi kan wasu batutuwan da suka shafi shirye-shiryen taron ministocin harkokin kasuwanci na kasashen WTO karo na 13 ( MC13) da sauransu.

Wang Wentao ya gana ne da Ngozi Iweala a jiya Jumma’a, yayin da yake halartar taron ministocin kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin Asiya da tekun Pasific (APEC) a birnin Detroit na kasar Amurka.
A yayin ganawar, Okonjo-Iweala ta yaba da kyakkyawar rawar da kasar Sin take takawa a cikin kungiyar WTO, inda ta bayyana fatan ganin kasar Sin ta ci gaba da ba da jagoranci wajen cimma nasara a yayin taron MC13.

A nasa bangaren, Wang Wentao ya bayyana cewa, kasarsa tana aiwatar da ainihin ra’ayin kasancewar bangarori da dama, kana tana taka rawar gani wajen yin gyare-gyare a WTO, kuma za ta gudanar da ayyuka masu amfani da za su bayar da gudummawa ga cimma nasarar taron MC13.

A yayin taron dandalin, Wang Wentao ya kuma gana da wakiliyar kasuwanci ta kasar Amurka Katherine Tai, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayi sosai bisa gaskiya kuma a zahiri, kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Amurka da Sin, da kuma batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na bangarori da dama da ke jan hankulansu duka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Ce Ta Daya A Noman Gero Ta Uku A Noman Gyada A Duniya – Farfesa Gaya

Next Post

Wace Kungiya Ce Za Ta Iya Taka Wa Man City Burki?

Related

Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi
Daga Birnin Sin

6 hours ago
Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar

7 hours ago
Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya

8 hours ago
Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma
Daga Birnin Sin

Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma

9 hours ago
Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5

10 hours ago
Xi Ya Bukaci Kungiyoyin Matasa Da Dalibai Su Zurfafa Gyare-Gyare Da Kirkire-Kirkire Don Samun Sabbin Nasarori

11 hours ago
Next Post
Wace Kungiya Ce Za Ta Iya Taka Wa Man City Burki?

Wace Kungiya Ce Za Ta Iya Taka Wa Man City Burki?

LABARAI MASU NASABA

Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi

Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi

July 2, 2025
Gwamnatin Kano Ta Haramta Shigo Ƙarafu Daga Arewa maso Gabas

Gwamnatin Kano Ta Haramta Shigo Ƙarafu Daga Arewa maso Gabas

July 2, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar

Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar

July 2, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya

Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya

July 2, 2025
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano

July 2, 2025
Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma

Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma

July 2, 2025
Abubakar Malami Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC

Abubakar Malami Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC

July 2, 2025
Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5

Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5

July 2, 2025
Rukunin Ƴan APC A Kano Sun Nemi A Rushe Jagorancin Jam’iyyar A Jihar

Rukunin Ƴan APC A Kano Sun Nemi A Rushe Jagorancin Jam’iyyar A Jihar

July 2, 2025
Xi Ya Bukaci Kungiyoyin Matasa Da Dalibai Su Zurfafa Gyare-Gyare Da Kirkire-Kirkire Don Samun Sabbin Nasarori

Xi Ya Bukaci Kungiyoyin Matasa Da Dalibai Su Zurfafa Gyare-Gyare Da Kirkire-Kirkire Don Samun Sabbin Nasarori

July 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci