A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 65, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
A cikin sakonsa Wang Yi ya bayyana cewa, cikin shekaru 65, an raya dangantaka tsakanin Sin da Ghana yadda ya kamata, kana an karfafa imani da juna kan harkokin siyasa, tare da samun manyan nasarori a hadin gwiwarsu ta fannoni daban daban. Kazalika, sassan biyu sun goyi bayan juna a fannin kulawa da harkokin kasa da kasa.
Wang Yi ya ce, ana fatan yin kokari tare da minista Ablakwa, wajen kara fadada mu’ammala a tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu, da goyon bayan juna, da aiwatar da manufofi da aka amince da su, a gun taron koli na Beijing, na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, don sa kaimi ga daga dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Ghana zuwa sabon matsayi.
A nasa bangare, minista Ablakwa ya bayyana cewa, kasar Ghana na godewa Sin, bisa samar mata da gudummawa, da goyon baya a fannonin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Ya ce an samu manyan nasarori a fannin hadin gwiwar sassan biyu karkashin tsarin dandalin FOCAC, wanda hakan ya samar da babbar gudummawa ga kasashen Afirka ciki har da Ghana, wajen inganta karfinsu na samun ci gaba, kuma hakan zai amfani jama’ar kasashen Afirka baki daya. Bugu da kari, kasar Ghana tana fatan kokartawa tare da kasar Sin, wajen sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare yadda ya kamata. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp