Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Yana mai cewa, an fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu da wuri, inda aka samu sakamako da dama, kuma tana da babban tasiri, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu.
- Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya
- Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024
Kazalika, dangantakar Sin da Japan da Koriya ta Kudu tana kara bunkasa, za a kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Bugu da kari, hadin gwiwarsu na kara zurfafa, kasashen yankin za su kara kaimi wajen tunkarar kalubale daban daban daga waje.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Japan da Koriya ta Kudu, wajen kafa sahihiyar ra’ayi game da tarihin yakin duniya na biyu, da kiyaye tsarin bangarori daban daban, da kiyaye muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a tsarin kasa da kasa, da ci gaba da inganta hadin gwiwa, da ba da gudummawa ga samun zaman lafiya da wadata a shiyyar da duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp