Jiya Litinin, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron zangon farko na ganawar ministocin harkokin wajen kasashen BRICS, wanda aka gudanar a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
A yayin taron, Wang Yi ya bayyana matsayin kasar Sin game da batun kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka, da kiyaye dangantakar ciniki tsakanin bangarori daban daban. Ya ce, dangantakar cude-ni-in-cude-ka ita ce tushen kiyaye tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, amma, kasar Amurka ta nuna ra’ayin son kai, tare da mai da moriyar kanta a gaban sauran kasashen duniya, lamarin da ya kawo barazana ga bunkasuwar dangantaka tsakanin sassan kasa da kasa.
- Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
- Gwamnatin Yobe Na Ƙoƙarin Inganta Tsaro – Hon. Idi Gubana
Haka kuma, Wang Yi ya jaddada cewa, “Abu mafi muhimmanci dake gabanmu a halin yanzu, shi ne kare tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, duba da cewa neman sulhu da ja da baya kan batun, za su zamo wata dama ga masu son cin zali. Don haka ya kamata mambobin kasashen BRICS su hada kansu, tare da yaki da kariyar ciniki, da kiyaye tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, bisa manufofin duniya da kungiyar WTO, ta yadda za a inganta ‘yancin kai na gudanar da harkokin ciniki.
Ministan harkokin wajen kasar Brazil Mauro Vieira ne ya jagoranci wannan taro, inda bangarori daban daban suka tattaunawa kan yadda kasashen BRICS za su karfafa zaman lafiya da tsaron duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp